“Mun Sauke Nauyi: Daurawa Ya Tona Abin da Suka Fadawa Shugabanni Kan Zanga Zanga

“Mun Sauke Nauyi: Daurawa Ya Tona Abin da Suka Fadawa Shugabanni Kan Zanga Zanga

  • Yain da ake ta shirin fita zanga-zanga a Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana abin da suka fadawa shugabanni
  • Daurawa ya ce duk abin da ya kamata su fada sun fada inda ya ce idan wani abu ya faru to laifin shugabanni ne ko kuma na matasa
  • Shehin malamin ya bayyana haka yayin da ake ta zargin malaman addini ba su yi wani kokari ba wurin isar da sako ga shugabanni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana abubuwan da suka fadawa Shugaba Bola Tinubu kan halin da ake ciki.

Sheikh Aminu Daurawa ya ce sun sauke nauyi daga bangarensu wurin tabbatar da fadawa shugaban gaskiya kan halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

"Ka tsayar da komai tukun": Sheikh Guruntum ya ja hankalin Tinubu kan halin kunci

Sheikh Daurawa ya bayyana yadda suka yi da shugabanni
Sheikh Aminu Daurawa ya ce sun sauke nauyi kan isar da sako ga shugabanni. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Asali: Facebook

Zanga-zanga: Sheikh Daurawa ya shawarci shugabbanni

Shehin Malamin ya bayyana haka ne a yau Alhamis 25 ga watan Yulin 2024 a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daurawa ya ce sun kuma yi kokarin fadawa matasan Najeriya abin da ya kamata su yi dangane da shirin zanga-zanga.

Ya ce idan har wani abu ya faru to tabbas ko an samu matsala ne daga bangaren shugabannin ko kuma matasan Najeriya.

Daurawa ya gargadi matasa kan zanga-zanga

"Mun sauke nauyi, mun je mun fadawa shugabanni abin da ya kamata su yi inda muka fada musu lallai su zauna da matasa."
"Mun fada musu su ji damuwarsu kuma su dauki mataki na gaggawa kuma na gaskiya wanda zai fara aiki nan take."
"Kuma mun fadawa matasa abin da ya kamata su yi, idan wani abu ya faru, to dayan biyu ne ko dai shugabanni ba su yi abin da ya kamata ba ko kuma matasa."

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Malamin Musulunci ya bukaci fara 'Alkunut', ya nemo mafita ga talakawa

- Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Sheikh Mansur Yelwa ya shawarci malaman Musulunci

Kun ji cewa Sheikh Mansur Isa Yelwa ya bayyana abin da ya kamata malaman Musulunci su yi musamman a wannan yanayi da ake ciki.

Mansur Yelwa ya ce ya kamata malamai su kira mabiyansu domin fara 'Alkunut" a masallatai domin samun saukin rayuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.