Shugaban Cibiyar NERDC da Aka Nada Tun Zamanin Buhari, Farfesa Junaidu Ya Rasu

Shugaban Cibiyar NERDC da Aka Nada Tun Zamanin Buhari, Farfesa Junaidu Ya Rasu

  • Rahotanni da muke samu yanzu na nuni da cewa shugaban cibiyar nazari da bunkasa ilimi ta kasa, Farfesa Ismail Junaidu ya rasu
  • An ruwaito cewa Farfesa Ismail Junaidu, ya rasu ne a jihar Yobe inda yake halartar taron kwamitin tuntuba kan ilimi (JCCE)
  • A halin da ake ciki kuma, an dauki gawar shugaban NERDC zuwa Katsina domin yi masa sutura kamar yadda addini ya tanada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Yobe - Sakataren zartarwa na cibiyar nazari da bunkasa Ilimi ta kasa (NERDC), Farfesa Ismail Junaidu, ya rasu.

Rahotanni sun bayyana cewa Junaidu ya rasu ne da sanyin safiyar Alhamis a garin Damaturu na jihar Yobe, inda yake halartar taron kwamitin tuntuba kan ilimi (JCCE).

Kara karanta wannan

Sakataren APC ya gano 'kuskure' a rahoton gwamnati kan tsadar kayayyaki a Najeriya

Shugaban cibiyar NERDC, Farfesa Ismail Junaidu ya rasu
Allah ya yiwa Farfesa Ismail Junaidu, shugaban cibiyar NERDC rasuwa a Yobe. Hoto: psin.gov.ng
Asali: UGC

Shugaban NERDC ya kwanta dama

Har yanzu ba a tantance musabbabin rasuwar ba, amma wata majiyar Daliy Trust da ba ta so a bayyana sunanta ta ce marigayin ya yanke jiki ne ya fadi matacce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, wani jami'in cibiyar NERDC ya musanta wannan ikirarin, ya ce Farfesa Junaidu ba yanke jiki ya yi ya fadi ba.

"Ba yanke jiki ya yi ya fadi ba, lokacin mutuwarsa ne dai ya yi."

- Inji jami'in NERDC.

A halin da ake ciki kuma, an dauki gawar shugaban NERDC zuwa Katsina domin yi masa sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Buhari ya amince da nadin Farfesa Junaidu

Jaridar ThisDay, a wani rahoto da ta wallafa a 2 ga watan Agustar 2016 ta ce shugaban kasa na wancan lokaci, Muhammadu Buhari ya amince da nadin Farfesa Junaidu matsayin shugaban NERDC.

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Tinubu, tsohon kakakin kamfen Atiku ya fice daga PDP zuwa APC

A wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai na ma'aikatar ilimi (na wancan lokacin) Benjamin Goong ya fitar, ma'aikatar ta ce Farfesa Junaidu ya kama aiki 1 ga Agusta.

Wannan na zuwa ne bayan da Shugaba Buhari ya sanar da korar dukkanin shugabannin hukumomi da cibiyoyin ilimin kasar har su 17 tare da nada wasu sababbi.

Tsohon shugaban hukumar EFCC ya rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Lamorde ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 61.

Marigayin ya rasu ne a kasar Masar yayin da ya je domin yin jinya kamar yadda aka sanar da safiyar Lahadi 26 ga watan Mayu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.