Masana sun bayyana ra'ayin mayar da yaren Hausa harshen kasa gaba daya

Masana sun bayyana ra'ayin mayar da yaren Hausa harshen kasa gaba daya

A ranar talata zuwa Alhamis din makon da ya gabata ne a ka shirya taron duniya na masana harshen Hausa inda su ka bayyana ra'ayoyinsu na mayar da harshen Hausa a matsayin na kasa baki daya duba da cewa Hausawa suka assasa kafuwar Najeriya

Masana harsunan Afirka wadanda su ka halarci babban taron duniya a kan harshen Hausa da aka gudanar a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya cikin jihar Kaduna, sun bukaci a fara amfani da harshen Hausa a matsayin harshen kasa a Najeriya, musamman ganin yadda ya samu karbuwa a sassan kasar nan da Afirka da duniya baki daya.

Taron mai taken ‘kasar Hausa: Jiya da Yau da Gobe’ , Sashen Nazarin Al’adu Da Harsunan Afirka na Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya ne ya shirya daga Talata zuwa Alhamis din makon da ya gabata.

Taron ya hado masana harsuna daga sassan duniya, inda suka ce bisa la’akari da yadda harshen ya samu karbuwa, lokaci ya yi da za a mai da shi ya zama harshen kasa, gwamnati ta rika gudanar da al’amuranta na yau da kullum da shi, kuma hakan zai taimaka wajen kawo hadin kan kasa da bunkasa tattalin arziki da saukaka al’amuran mulki da siyasa a kasar nan.

Masana sun bayyana ra'ayin mayar da yaren Hausa harshen kasa gaba daya
Masana sun bayyana ra'ayin mayar da yaren Hausa harshen kasa gaba daya

Shugaban taron, Mai shari’a Umaru Abdullahi, Walin Hausa ya kalubalanci masana harshen Hausa a kan su maida hankali wajen gudanar da bincike ta yadda harshen zai kara bunkasa a daina ganin al’ummar Hausawa a matsayin cima-zaune, alhalin su ne suka gina kasar nan tare da tabbatar da hadin kanta, balle kuma yanzu da harshen ya bunkasa, ya buwaya a duniya.

A jawabin Shehun Malamin Hausa, Farfesa Dandatti Abdulkadir, ya bayyana yadda harshen ya samu tagomashi a duniya inda manyan kasashe irin su Birtaniya da Amurka da Jamus da Faransa da Sin da sauransu ke amfani da shi wajen bunkasa al'amuransu da kasashen Afirka.

Dandatti ya yi kira ga gwamnonin Arewa da sauran ma su fada a ji a kasar nan da su yi gaggawar gabatar da harshen Hausa a matsayin harshen gudanar da harkoki a jihohin na arewacin kasar nan, kuma a yi yunkurin mayar da shi ya zamto harshen da ake amfani da shi a kasa gaba daya.

“Harshen Hausa ya bunkasa a duniya, yana daya daga cikin harsunan Afirka na sahun farko da gidan rediyon BBC ya fara amfani da shi wajen watsa labarai a duniya, kuma yana da miliyoyin masu saurare a duk fadin duniya. Harshen yana da duk abubuwan da ake bukata domin zama harshen kasa. Don haka, ya kamata ’yan siyasarmu, musamman gwamnonin Arewa su sanya ya zama harshen hukuma a duk fadin Arewa, sannan su yi kokarin ganin ya zama harshen kasa cikin gaggawa,” inji Farfesa dandatti.

Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Ibrahim Garba, ya bayyana bukatar a yi kokarin tabbatar da harshen Hausa ya zama harshen kasa, musamman saboda yadda ya bunkasa kuma ya mamaye ko’ina a Najeriya da nahiyar Afirka. Ya ce: “Mu a nan Jami’ar Ahmadu Bello, mun amince cewa harshen Hausa yana da kima da daraja, yadda ya karade ko’ina, musamman makwabtan kasashe da al’ummomin Afirka. Harshe ne na koyo da koyarwa kuma yana taimakawa wajen samar da hadin kai a tsakanin al’umma daban-daban.”

KU KARANTA: Aikin Hajji: Fiye da rabi na maniyyatan Jigawa ba za su je aikin Hajjin bana ba

A jawabin, Shugaban Sashen Nazarin Al’adu da Harsunan Afirka na Jami’ar, Dokta Salisu Garba Kargi, ya bayyana dalilin gudanar da wannan taro shine don a wayar da kawunan jama'ar duniya a kan irin matakin da harshe na Hausa ya taka. “Sanin kowa ne cewa irin mataki da munzalin da harshen hausa ya taka, nuni ne da alamar cewa ya isa zama harshen kasa, domin a rinka harkokin shugabanci da gudanar da al'amura da yaren a kasar nan.

Wannan ya sa aka shirya taron ranar Talata, 26 ga Nuwamba, 2016 domin kara tabbatar da matsayin harshen Hausa ba a Najeriya kawai ba, har da Nahiyar Afirka baki daya. Wancan taro ne ya bukaci lallai a kira babban taro na duniya, wanda zai game fannoni daban-daban don samar da cikakken bayani a kan al’ummar Hausawa da ire-iren albarkatun da suke jibge a cikin kasarsu,” inji Dokta Kargi.

Akwai ire-iren masana wadanda ba a bari a baya ba wajen gabatar da na su takardun da kara nuna irin munzali da matakin da Harshen na Hausa ya kai, wadanda su ka hadar da: Farfesa Isma’ila Junaidu, Babban Sakataren Hukumar Tsara Manhajar Karatu ta kasa (NERDC) da ke Abuja da Farfesa Al-Amin Abu Manga, na Cibiyar Nazarin Al’amuran nahiyar Afrika da Asiya a Jami’ar Khartoum dake kasar Sudan da Farfesa Nina Pawlak ta Cibiyar Nazarin kasashen Gabas da Sashen Harsuna da Al’adun Afirka ta Jami’ar Warsaw na kasar Poland da kuma Malam Abubakar Mahamman, Shugaban kungiyar Marubuta Harsunan kasa dake garin Yamai na kasar Nijar.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel