Sultan da Manyan Sarakunan Gargajiya Sun Sanya Labule da Tinubu, Bayanai Sun Fito
- Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zanga-zanga, Sarkin Musulmi ya jagoranci sarakunan gargajiya zuwa fadar Bola Tinubu
- Sultan ya jagoranci sarakunan ne ciki har da Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi domin ganawa a fadar Tinubu da ke Abuja
- Duk da ba a bayyana musabbabin ganawar ba, wasu na ganin bai rasa nasaba da shirin zanga-zanga da halin kunci da ake ciki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya samu isa fadar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu domin wata ganawa.
Mai alfarma Sultan ya jagoranci sauran manyan sarakunan gargajiya a Najeriya domin fara ganawar a yau Alhamis 25 ga watan Yulin 2024.
Sultan, sarakunan gargajiya suna ganawa da Tinubu
Tribune ta tattaro cewa Sultan da sauran sarakunan sun iso fadar a cikin wata motar bas a ganawar da aka fara da misalin karfe 2:30 na rana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ganawar akwai manyan sarakunan gargajiya ciki har da Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi.
Sai dai ba a tabbatar da musabbanin ganawar Tinubu da sarakunan gargajiya ba har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, cewar Punch.
Rahotannin sun tabbatar da cewa hakan bai rasa nasaba da halin kunci da ake ciki a kasar da mawuyacin tsadar rayuwa.
Har ila yau, wasu na ganin ganawar na da alaka da shirin zanga-zanga da matasa ke kokarin yi a fadin kasar baki daya.
Manyan gwamnati wajen ganawar Sultan-Tinubu
Daga cikin wadanda suka halarci ganawar akwai mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume.
Sauran sun hada da mai ba Tinubu shawara a harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da kuma Babban Sifetan 'yan sanda, Kayode Igbetokun da gwamnoni da kuma Ministoci.
Tinubu ya gana da gwamnonin APC
Kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da wasu gwamnonin jam'iyyar APC a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.
Taron ya biyo bayan dakatar da zaman majalisar zartaswa ta ƙasa da aka shirya yi a ranar Alhamis, 25 ga watan Yulin 2024.
Shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodinma shi ne ya jagoranci gwamnonin zuwa ofishin shugaban ƙasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng