Riƙakken 'Dan Damfara da Ya Yi Shekaru 2 Yana Karyar Shi Soja ne Ya Shiga Hannu
- Rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Bauchi ta kama wani mutum da yake karyar shi soja ne domin ya damfari mutane
- Mutumin mai suna Aminu Muhammad ya shiga hannu ne bayan yan sanda da ke karamar hukumar Tafawa Balewa sun kama shi
- Yan sanda sun bayyana tulin kudin da Aminu Muhammad ya damfari wani da inda ya samo kayan sojojin Najeriya yake aiki da su
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta cafke wani matashi mai suna Aminu Muhammad da yake karyar shi soja ne.
Aminu Muhammad ya kasance yana damfarar mutane kudi kafin ya shiga hannun yan sanda a karamar hukumar Tafawa Balewa a Bauchi.
Legit ta gano yadda aka kama Aminu Muhammad ne a cikin sakon da rundunar yan sanda ta wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bauchi: Yan sanda sun kama sojan bogi
A ranar 22 ga watan Yuli yan sanda a jihar Bauchi suka kama Aminu Muhammad da yake karyar shi soja ne.
Bincike ya nuna cewa Aminu Muhammad ya shafe shekaru biyu yana cutar mutane da sunan shi sojan Najeriya ne.
Dalilin kama sojan bogi a jihar Bauchi
Jaridar Leadership ta wallafa cewa Aminu Muhammad ya karbi makudan kudi kimanin N210,000 da suna zai samawa wani aikin soja.
Biyo bayan gaza samawa mutumin aiki ne sai ya kai karar Aminu wajen yan sanda a Tafawa Balewa kuma hakan ya jawo nasarar cafke sojan bogin.
Aminu bai taba shiga aikin soja ba
Bincike ya nuna cewa dan damfarar bai taba shiga aikin soja ba sai dai ya samu kayan sojoji ne a wajen wani abokinsa da jami'in tsaro ne.
A yanzu haka kwamishinan yan sanda a Bauchi, CP Ahmed Mohammed Wakil ya tura sojan bogin sashen bincike domin kammala bincikensa.
An kama dan sandan bogi a Legas
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sandan jihar Legas ta kama wani mutum mai suna Charles Chukwudi da ke damfarar mutane da sunan aikin dan sanda.
An kama mutumin ne dauke da kayayyakin da suka shafi aikin yan sanda da kotu da yake amfani da su wajen damfarar mutane.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng