Minista Ya Lallashi 'Yan Zanga Zanga, Wike Ya yi Alkawari Shugaba Tinubu Zai Kawar da Yunwa

Minista Ya Lallashi 'Yan Zanga Zanga, Wike Ya yi Alkawari Shugaba Tinubu Zai Kawar da Yunwa

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya roki mazauna birnin su yi hakuri tare da kauracewa zanga-zanga
  • Nyesom Wike ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya na daukar matakan kawar da yunwa da ta dame su
  • Ministan na wannan batu ne a lokacin da shugaba Bola Tinubu ya ba wa 'yan Najeriya hakuri tare da cewa za a gyara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike ya shawarci mazauna babban birnin tarayya da su ajiye maganar zanga-zangar gama gari da aka shirya gudanarwa a daga ranar 1-15 Agusta, 2024.

Kara karanta wannan

Sakataren APC ya gano 'kuskure' a rahoton gwamnati kan tsadar kayayyaki a Najeriya

Nyesom Wike ya bayyana haka ne a ranar Alhamis lokacin da ya ke duba aikin titin Saburi a Abuja, inda ya bayar da tabbacin shugaban kasa, Bola Tinubu zai dauki mataki.

Tinubu
Minista Wike ya ce shugaba Tinubu na shirin kawar da yunwa Hoto: Ajuri Ngelale (Facebook)
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa ‘yan Najeriya sun bayyana aniyarsu ta shiga zanga-zangar lumana domin jan hankalin gwamnati a kan matsalolin da su ke fuskanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Bola Tinubu zai gyara,” Wike

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai dauki matakin magance matsalolin kasa, musamman yunwa Daily Post ta wallafa wannan.

Ministan ya shawarci ‘yan Najeriya su yi hakuri, domin yunwa da ake fama da ita yanzu mai wucewa ce ganin yadda Tinubu ke aiki ba dare ba rana.

“Kar ku yi fushi ku shiga zanga-zanga, saboda zanga-zanga ba za ta magance matsalar ba. Gwamnati ta san akwai yunwa, shi yasa ta ke aiki tukuru domin magance ta.”

Kara karanta wannan

Tinubu: Fitaccen Sarki ya aika muhimmin saƙo ga matasa masu shirin yin zanga zanga

-Ministan Abuja, Nyesom Wike

Tinubu ya dauki matakin hana zanga-zanga

A baya mun ruwaito cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dauki matakin da zai dakile aniyar jama'ar kasar nan ta fita zanga-zangar gama-gari a watan Agusta.

Tun a ranar Talata shugaban ya ba wa matasan Najeriya hakuri, inda ya bayyana cewa zai dauki matakin da za su gamsu da shi domin kin fita zanga-zangar da ake sa ran yi na kwanaki 15.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.