Sojoji Sun Ragargaji Yan Bindigan da Suka Fitini Kaduna, Sun Kashe Manyan Miyagu

Sojoji Sun Ragargaji Yan Bindigan da Suka Fitini Kaduna, Sun Kashe Manyan Miyagu

  • Rundunar sojin Najeriya ta samu nasara kan wasu manyan yan bindiga da suka fitini al'umma a jihar Kaduna
  • Rahotanni sun nuna cewa sojojin Najeriya sun yi musayar wuta da miyagun ne kafin samun nasara a kansu
  • Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ta kwato makamai da kudi a wajen yan ta'addar bayan ta hallaka su

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Rundunar sojin Najeriya ta yi musayar wuta da wasu yan bindiga a kananan hukumomin jihar Kaduna.

Rahotanni sun nuna cewa sojojin Najeriya sun samu nasara kan miyagun ne bayan sun yi musayar wuta.

Sojoji
Sojoji sun kashe yan ta'adda a Kaduna. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Getty Images

Sojojin Najeriya sun bayyana kayan da suka kwato wajen yan ta'addar a wani sako da suka wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Sarakuna sun shiga uku, an bukaci Gwamna ya dauki tsattsauran mataki kansu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun samu bayanan sirrin 'yan bindiga

A jiya Laraba, 24 ga watan Yuli ne sojojin Najeriya suka samu bayanan sirri kan ayyukan wasu yan bindiga a jihar Kaduna.

Biyo bayan samun bayanan, sojojin sun tunkari miyagun inda suka gwabza fada a hanyar Tasha-Bwari da ke tsakanin Gurara da Kagarko.

Dakarun Sojoji sun kashe yan bindiga

A yayin da sojojin Najeriya suka tunkari yan ta'addar sun yi musayar wuta wanda hakan ya jawo mutuwar yan ta'adda biyu.

Haka zalika wasu daga cikin yan ta'addar sun gudu da munanan raunuka bayan kuma sun watsar da makaman da suke ta'addanci da su.

Sojoji sun kwato makaman yan bindiga

Bayan artabun, rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar kwato makamai ciki har da bindiga kirar AK47, tulin harsashi da adduna guda biyu.

Haka zalika rundunar sojin Najeriya ta kwato wayoyin hannun guda biyu da tsabar kudi kimanin N80,000 a wajen yan ta'addar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun samu gagarumar nasara a kan Boko Haram bayan gwabza kazamin fada

Jami'an Sojoji sun ceto mutane a Borno

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta samu gagarumar nasara kan yan ta'addan Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa rundunar sojin Najeriya ta fafata a wani kazamin fada da yan ta'addar kafin samun nasarar da ceto mata da yara kanana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng