Sakataren APC Ya Gano 'Kuskure' a Rahoton Gwamnati Kan Tsadar Kayayyaki a Najeriya
- Sakataren APC na kasa, Ajibola Basiru ya musanta rahoton cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya kai matakin 'intaha'
- A yayin da Ajibola Basiru ya yarda cewa Najeriya na fuskantar kalubalen tattalin arziki sai dai ya ce rahoton NBS na zuzuta lamarin ne
- Tsohon kakakin majalisar dattawan ya ce gwamnati Shugaba Bola Tinubu na iya kokarinta domin magance matsalar abinci
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ajibola Basiru, sakataren jam’iyyar APC na kasa, ya nuna rashin amincewa da alkaluman hauhawar farashin kayayyaki da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar.
Ajibola Basiru ya bayyana hakan a daidai lokacin da ake kira da a gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a ranar 1 ga watan Agusta.
Sakataren APC ya yi maganar rahoton NBS
Da ya ke magana a Channels TV, Basiru ya ce duk da cewa tattalin arzikin kasa na fuskantar kalubale, amma tabarbarewar ba ta kai haka ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin hirar, Seun Okinbaloye, mai gabatar da shirye-shirye, ya bijiro da alkaluman tsadar kayayyaki daga watan Yuni 2023 da Yuli 2024 wanda NBS ta fitar.
Ajibola, tsohon kakakin majalisar dattawa, ya ce bai amince da alkaluman NBS ba. Amma dai ya ce tabbas kasar na fuskantar "hauhawar farashin kayayyaki".
"Gwamnatin Tinubu na kokarin gyara" - Ajibola
Sakataren jam'iyya mai mulkin ya ce:
"Na san cewa akwai kalubalen hauhawar farashin kayayyaki amma bai kai wannan matakin ba. Ban yarda da wannan rahoton ba.
"Na san cewa akwai kalubalen hauhawar farashin kayayyaki kuma a matsayinmu na gwamnati, muna kokarin magance kalubalen."
Tsohon kakakin majalisar dattawan ya ce gwamnatin da Shugaba Bola Tinubu ke jagoranta na samar da matakan magance matsalar abinci.
Kalli tattaunawar a nan kasa:
NBS ta fitar da rahoton farashin kayayyaki
Tun da fari, mun ruwaito cewa hukumar NBS ta ce an samu tashin farashin wake, shinkafa, tumatur, garin kwaki, doya a cikin watan Yunin da ya wuce.
NBS ta ce farashin tumatur ya tashi da kashi 55.67% idan aka kwatanta da Mayun da ya wuce lamarin da ta ce farashin na lulawa sama ne babu kakkautawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng