“Ba Mu San Dalilinku Ba”: Gwamnonin APC Sun Tura Sako ga Matasa Kan Zanga Zanga

“Ba Mu San Dalilinku Ba”: Gwamnonin APC Sun Tura Sako ga Matasa Kan Zanga Zanga

  • Yayin da ake shirin gudanar da zanga-zanga a Najeriya, kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC ta tura sako ga matasan kasar
  • Kungiyar ta ce babu dalilin yin zanga-zanga a daidai wannan lokaci inda ta ce ba ta san musabbabin zanga-zangar ba
  • Shugaban gwamnonin APC, Hope Uzodinma shi ne ya bayyana haka inda ya ce su na kokarin shawo kan lamuran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnonin jam'iyyar APC sun bayyana damuwa kan yadda matasa ke shirin gudanar da zanga-zanga a kasar.

Gwamnonin suka ce rashin ilimi ne musabbabin wannan zanga-zanga duk da sun sani an fada wani yanayi a kasar.

Gwamnonin APC sun tura sako ga matasan Najeriya
Gwamnonin APC a Najeriya sun bukaci zama da masu zanga-zanga. Hoto: @NGFSecretariat.
Asali: Twitter

Zanga-zanga: Gwamnonin APC sun shawarci matasa

Kara karanta wannan

Gwamnonin jihohi 36 sun yi magana kan zanga zangar da matasa ke shirin yi

Shugaban gwamnonin APC, Hope Uzodinma shi ya bayyana haka bayan taron kungiyar NGF, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uzodinma ya ce kwata-kwata ba su san dalilin shirya zanga-zangar ba da matasa ke kokarin yi inda ya ce sun bukaci zama da su.

Ya ce gwamnonin sun himmatu wurin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a kasa da kuma samar da ingantacciyar rayuwa, Vanguard ta tattaro.

"Ba mu san musabbabin shirya wannan zanga-zanga ba da matasa ke yi, muna gayyatarsu su zo mu zauna domin samun mafita."
"A matsayinmu na kungiya, mun himmatu wurin tabbatar da inganta rayuwar 'yan Najeriya da samar da ayyuka ga matasa."

- Hope Uzodinma

Uzodinma ya roki matasa masu shirin zanga-zanga

Gwamna Uzodinma ya ce ko kadan bai dace ba a gudanar da zanga-zanga a dai-dai wannan lokaci da ake ciki.

Kara karanta wannan

Zanga zangar gama gari: Direbobin tankar fetur sun fitar da matsaya a Najeriya

Ya roki matasan da su janye shirinsu na yin zanga-zanga domin samun damar kawo karshen matsalolin da ake ciki.

Gwamnoni sun shiga ganawa ta musamman

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar gwamnonin Najeriya ta NGF ta shiga ganawar gaggawa yayin da ake shirin gudanar da zanga-zanga.

A ganawar da aka gudanar, an tattauna batutuwa da dama da suka hada da zanga-zanga da kuma mafi karancin albashin ma'aikata.

Wannan shi ne ganawar farko da kungiyar ta yi tun bayan amincewa da mafi karancin albashin N70,000 da Bola Tinubu ya yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.