Gwamnan APC Ya Tsure, Ya Bayyana Fargabarsa a Kan Shirin Zanga Zangar Lumuna
- Bayan dagewa da masu shirin zanga-zanga su ka yi a kan lallai sai sun nuna bacin ransu ga gwamnati, gwamnatin Legas ta bayyana fargaba
- Sakatariyar gwamnatin jihar, Barista Bimbola Salu Hundeyin ta bayyana cewa akwai fargabar za a iya jawo asarar dukiyoyi da rayukan jama'a
- Ta ce bai kamata a gudanar da zanga-zanga a jihar Legas ba, ganin yadda gwamnatin ta yi kokari wajen inganta rayuwar mazauna cikinta
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Legas - Yayin da gwamnati ta ga yadda jama'ar kasar nan su ka dage a kan tsunduma zanga-zanga, gwamnatin jihar Legas ta fara kiraye-kiraye gudanar da ita cikin lumana.
Gwamnatin ta gargadi wadanda ke da niyyar fitowa daga ranar 1 Agusta, 2024 domin yin zanga-zanga da su tabbata sun guji lalata kadarori ko tayar da hankula.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa jihar Legas ta bakin sakatariyar gwamnati, Barista Bimbola Salu Hundeyin ce ta yi gargadin yayin wani taro da sakatarorin kananan hukumomi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati ta shiga damuwa kan zanga zanga
Gwamnatin jihar Legas ta shiga damuwa a kan shirin zanga-zangar gama gari ta kwanaki 15 da wasu 'yan Najeriya ke shirin yi.
Sakatariyar gwamnatin jihar, Barista Bimbola Salu Hundeyin ce ta bayyana damuwar, inda ta ce akwai fargabar za a iya lalata dukiyoyi da jawo asarar rayuka, Daily Post ta wallafa.
Ta ce duk da cewa zanga-zanga 'yancin kowanne dan kasa ce, bai kamata a gudanar da ita a jihar Legas da ta yiwa jama'a aikin da ya kamata ba.
Zanga-zanga: Sanata Ndume ya shawarci Tinubu
A baya kun ji cewa Sanata mai wakiltar Kudancin Borno a majalisa, Ali Ndume ya shawarci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a kan yadda za ta gujewa faruwar zanga-zanga.
Sanata Ali Ndume ya nemi shugaban kasa da mukarrabansa su zauna a kan teburin sulhu da wakilan matasan kasar nan domin lalube mafita mafi sauki a maimakon zanga-zanga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng