Abba Kabir Ya Kaddamar da Muhimmin Aikin da Zai Inganta Yanayi da Noma a Kano
- Gwamnan Kano, mai girma Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da shirin dasa miliyoyin bishiyoyi a fadin jihar
- Gwamnatin Kano ta fadi dalilin fara dasa bishiyoyin da amfanin da al'umma za su samu daga aikin dasa itacen
- Abba Kabir Yusuf ya yi barazanar daukan mataki mai tsanani ga duk wanda aka samu ya sare bishiya a jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da shirin fara dasa bishiyoyi a fadin jihar Kano.
A jiya Laraba ne gwamnan tare da wasu jami'an gwamnatin jihar suka kaddamar da shirin tare da faɗin yadda shirin zai cigaba da gudana.
Legit ta tattaro bayanan da gwamnan ya yi ne a cikin wani sako da daraktan yada labaran Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bishiyoyi nawa Abba zai shuka?
A jiya Laraba Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da shirin dasa bishiyoyi na shekarar 2024 wanda za a shuka bishiyoyi har miliyan uku.
Hakan na cikin kudurin gwamantin Kano na dasa bishiyoyi miliyan 10 a mulkin Abba Kabir Yusuf na farko.
Dalilin dasa bishiyoyi a jihar Kano
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa shirin zai taimaka wajen rage dumamar yanayi a fadin jihar.
Haka zalika Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa aikin zai taimaka wajen inganta harkar noma da yakar zaizayar kasa.
Abba ya mika sako ga al'umma
Abba Kabir ya yi kira ga al'ummar jihar kan lura da bishiyoyin da kuma cewa za a hukunta duk wanda aka kama yana sare bishiya a jihar.
A karshe gwamna Ababa Kabir Yusuf ya ce za su saka yan makaranta, ma'ikata da yan kasuwa cikin shirin domin ingantasa.
Yan daba: Gwamna Abba ya yi gargadi
A wani rahoton, kun ji cewa yayin da gwamnatin Kano ke kokarin dakile matsalar 'yan daba, Gwamna Abba Kabir ya fusata kan sakin wasu da aka yi.
Gwamnan ya nuna bacin ransa inda ya ke zargin jam'iyyun adawa da hannu a sakin matasan bayan ya yi kokarin kawo karshen matsalar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng