Kwararowar hamada: Gwamna ya sanya kyautar naira dubu 100 ga duk mutumin daya dasa bishiya
Gwamnan jahar Yobe, Mai Mala Buni ya sanya kyautar N100,000 ga duk mutumin da yayi rajista da gwamnati, ya karbi irin bishiya, ya dasa bishiyar sa’annan ya yi dawainiya da ita tsawon shekara 1 cur!
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake kaddamar da rabon irin bishiyoyi a garin Damaturu, babban birnin jahar Yobe, inda yace ya kirkiro wannan tsari ne domin yaki da kwararowar hamada.
KU KARANTA: Adam Zango ya ciri tuta a matsayin jarumin da ya fi taimaka ma talakawa
Gwamnan yace manufar sanya kyautar shi ne domin baiwa jama’a kwarin gwiwa shiga a dama dasu a kokarin da gwamnati ke yin a tabbatar da tsaron muhalli, tare da kyautata ma duk wadanda suka taimaka wajen kawar da wannan babbar kalubale.
A jawabinsa, Gwamna Mala, wanda ya samu wakilcin mataimakin gwamna Idi Gubana yace: “Saninku ne jahar Yobe nada karancin bishiyoyi, haka zalika ga aikin manoma ma share fili, yanke bishiyoyi ba bisa ka’ida ba, da kuma hakar ma’adanai, dukkaninsu sun taimaka wajen lalata muhallanmu.”
Don haka gwamnan ya umarci sarakuna, hakimai da dagatai da suauran masu ruwa da tsaki dasu baiwa batun shuka bishiya muhimmanci. “Na umarci kananan hukumomi su kafa kwamitoci da zasu sanya idanu a kan masu aikin yanke itatuwa ba bisa ka’ida ba.
“Sa’annan su sanya idanu wajen tabbatar da da dabbaka dokokin kare muhalli domin samar da ingantaccen muhalli da kowa zai yi alfahari da shi.” Inji shi.
A wani labarin kuma, gwamnatin jahar Imo a karkashin jagorancin Gwamna Emeka Ihedioha ta bayyana cewa babu wanda ya isa ya sallami Fulani makiyaya daga jahar, don haka ya yi kira ga jama’a da suyi watsi da kashedin da wata kungiyar matasan ibo suka yi ga makiyaya dasu fice daga jahar cikin sa’o’i 24.
Kaakakin gwamnan jahar, Chibuike Onyeukwu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar inda yace kungiyar mai suna ‘South East Youth Leaders’ ba ta da hurumin yin magana da yawun al’ummar jahar ko gwamnatin jahar.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng