“Ka Tsayar da Komai Tukun”: Sheikh Guruntum Ya Ja Hankalin Tinubu Kan Halin Kunci

“Ka Tsayar da Komai Tukun”: Sheikh Guruntum Ya Ja Hankalin Tinubu Kan Halin Kunci

  • Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Tijjani Guruntum ya shawarci gwamnatin Bola Tinubu kan halin kunci da ake ciki
  • Sheikh Guruntum ya gargadi gwamnatin kan halin da ake ciki inda ya ce su tsayar da komai domin shawo kan matsalar
  • Malamin ya ce hanya daya ce wurin shawo kan masifar da ake ciki inda ya ce a dawo da tallafi kamar yadda aka cire

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi - Sheikh Ahmad Tijjani Guruntum ya tura muhimmin sako ga Shugaba Bola Tinubu kan halin kunci a Najeriya.

Shehin malamin ya ce ana cikin wani irin yanayi amma fa ta yadda aka hau ta nan ya kamata a sauko game da cire tallafi.

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Tinubu, tsohon kakakin kamfen Atiku ya fice daga PDP zuwa APC

Sheikh Guruntum ya gargadi Tinubu kan halin kunci a Najeriya
Sheikh Ahmad Tijjani Guruntum ya ba Bola Tinubu shawara kan halin kunci da ake ciki. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Mallam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum.
Asali: Facebook

Sheikh Guruntum ya ba Tinubu shawara

Sheikh Guruntum ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Laraba 24 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Muna kara kira ga gwamnati su yi abin da ya dace, kada su bar wannan matsalar da suke da hanyar maganceta ta zama babba."
"Yadda kuka ce 'fuel subsidy is gone' sai kuce 'fuel subsidy is back' magana ta kare, ta kare ko ba ta kare ba?."
"Dukiyar al'umma ce idan kai kace ga abin da kake so ko ga lissafinka idan jama'a suka ce ga yadda suke so sai ka yi, ba dimukradiyya ba kenan."
"Haka aka yaudari mutane cewa wasu kalilan ne suke cin moriyar tallafin talakawa ba su san amfaninsa ba, yanzu talaka ba zai gwammaci a dawo da tallafin tsirarun su ci gaba da ci ba?"

Kara karanta wannan

Kotu ta amince 'danuwan Yahaya Bello da ake zargi da badakalar N3bn ya tafi kasar waje

- Sheikh Tijjani Guruntum

Guruntum ya gargadi matasa kan zanga-zanga

Shehin Malamin har ila yau, ya shawarci matasa da su guji taba kayan mutane idan sun fita zanga-zanga inda ya ce amma ba su goyon baya kam.

Sheikh Guruntum ya ce ya kamata a tsayar da komai domin dawo da hankali wurin dakile matsalar da ake ciki na kuncin rayuwa.

Sheikh Mansur Yelwa ya shawarci malaman Musulunci

A wani labarin, kun ji cewa Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Farfesa Mansur Yelwa ya magantu kan zanga-zanga.

Malamin ya bukaci al'ummar Musulmai da shugabanni addinai da su sanar da fara yin 'Alkunut' domin samun sauki a fadin kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.