Tinubu da Wike Sun Shiga Uku, Iyalan Janar Sani Abacha Sun Maka Su a Kotu

Tinubu da Wike Sun Shiga Uku, Iyalan Janar Sani Abacha Sun Maka Su a Kotu

  • Iyalan marigayi Sani Abacha sun maka Shugaba Bola Tinubu da Ministan Abuja, Nyesom Wike a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja
  • Matar marigayin, Mariam Abacha da babban dansa, Mohammed Abacha sun dauki matakin ne bayan kwace kadarar mahaifinsu a Abuja
  • Suna zargin an siyar da kadarar ga wani kamfani mai suna Salamed Ventures Limited ba tare da saninsu ba ko kuma biyansu diyya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Matar marigayi Janar Sani Abacha da babban dansa, Mohammed Abacha sun maka Shugaba Bola Tinubu a kotu.

Mariam Abacha da iyalanta sun daukaka kara bayan Babbar Kotun Tarayya ta kwace kadarorin marigayin a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

An samu matsala a zaman Kotu kan shari'ar da Kwankwaso ya shigar da hukumar EFCC

Iyalan Abacha sun shiga kotu da Tinubu kan kwace kadara
Iyalan marigayi Janar Sani Abacha sun shiga kotu da Bola Tinubu kan kwace musu kadara ba bisa ka'ida ba. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Nigerian Government.
Asali: Facebook

Iyalan Abacha sun shiga kotu da Tinubu

Leadership ta tattaro cewa iyalan Marigayi Sani Abacha suna zargin an kwace kadarar da ke Maitama a Abuja ba bisa ka'ida ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin wadanda aka maka a kotun bayan Tinubu akwai Ministan Abuja, Nyesom Wike da wasu mutane biyu, cewar Vanguard,

Kadarar da ake zargin an kwace ba bisa ka'ida ba an siyar ga wani kamfani mai suna Salamed Ventures Limited ba tare da saninsu ko biyan diyya ba.

Korafin iyalan marigayi Abacha a Kotun Tarayya

Iyalan marigayin sun roki kotun da ta yi fatali da hukuncin Mai Shari'a, Peter Lifu a ranar 19 ga watan Mayun 2024 da ta gabata.

Lauyan wadanda ke karar, Reuben Atabo SAN ya gabatar da korafin inda yake kalubalantar hukuncin Mai Shari'a, Peter Lifu.

Ya ce alkalin kotun ya yi kuskure bayan ya dogara da sashe na 39 na dokokin mallakar filaye da ya sabawa matakin Kotun Daukaka Kara.

Kara karanta wannan

Abacha: Iyalin tsohon shugaban ƙasa sun yi rashin nasara, kotu ta yi hukunci bayan shekaru 9

Buba Galadima ya kare mulkin Abacha

A wani labarin, kun ji cewa jigon jam’iyyar NNPP, Buba Galadima ya bayyana cewa ba a taba samun nagartaccen shugaban kasa kamar Janar Sani Abacha ba.

Jigon NNPP wanda tsohon na hannun daman Muhammadu Buhari ne ya ce Abacha ko sisin kwabo bai dauka ba lokacin da ya ke mulkin soja.

Buba Galadima ya kara da cewa tun da ake shugabannin soji, Abacha har yanzu shi ne mafi nagarta da kasar ta yi a tarihi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.