Zanga Zanga: Malamin Musulunci Ya Bukaci Fara 'Alkunut', Ya Nemo Mafita ga Talakawa

Zanga Zanga: Malamin Musulunci Ya Bukaci Fara 'Alkunut', Ya Nemo Mafita ga Talakawa

  • Yayin da matasa ke shirin fita zanga-zanga a Najeriya, malamin Musulunci ya ba da muhimmiyar shawara ga matasa
  • Farfesa Mansur Yelwa ya bukaci shugabannin kungiyoyin addini da su kira mabiyansa domin fara 'Alkunut' a masallatai
  • Mansur Yelwa ya kuma shawarci dukkan Musulmai su tuba zuwa ga Allah da sauya halayensa domin neman biyan bukata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Farfesa Mansur Yelwa ya magantu kan zanga-zanga.

Malamin ya bukaci al'ummar Musulmai da shugabanni addinai da su sanar da fara yin 'Alkunut' domin samun sauki.

Malamin Musulunci ya yi kira da fara 'Alkunut' a Najeriya
Sheikh Farfesa Mansur Yelwa ya ba da shawarar fara 'Alkunut' a masallatai. Hoto: Professor Mansur Isa Yelwa.
Asali: Facebook

Farfesa Mansur Yelwa ya magantu kan zanga-zanga

Kara karanta wannan

A karon farko, Shugaba Tinubu ya yi magana kan matasa masu shirin yi masa zanga zanga

Wannan na kunshe ne a ciki wani faifan bidiyo da wani @jrnaib2 ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba 24 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesa Mansur ya kuma shawarci ƴan Najeriya da su tuba zuwa ga Ubangiji SWT wanda shi ne matakin farko.

Ya roki shugabannin kungiyoyin addinai da su sanar da mabiyansa domin fara 'Alkunut' a masallatai domin dakile fita zanga-zanga.

Zanga-zanga: Malamin Musulunci ya kawo mafita

"Na yi kokarin tuntubar shugabannin addini ko malamai ban same su ba, ina kira da su umarci dukkan Musulmi a dauki 'Alkunut' ya zama shi ne matsayar Musulmi madadin zanga-zanga."
"Ina kira da su ba da umarni Musulmi su shirya za a fara 'Alkunut' lokaci kaza da kuma sakawa mutane tuba da neman yafiyar Ubangiji."
"Saboda neman yafiyar Ubangiji shi ne maganin kowace matsala da damuwa kuma Allah ya yi alkawarin saukar da ni'ima da wadata ga wadanda suka nemi yafiya."

Kara karanta wannan

"Kowa a fusace ya ke": NLC ta ba Tinubu mafita kan shirin zanga zanga

- Sheikh Mansur Yelwa

Malami ya soki Tinubu kan tallafin shinkafa

A wani labarin, kun ji cewa malamin Musulunci a Gombe, Sheikh Adam Muhammad Albaniy ya caccaki tsarin raba tirelolin shinkafa.

Albanin Gombe ya ce wannan ba shi ne mafita ba abin da ya kamata kawai shi ne dawo da tallafin man fetur kamar yadda aka cire.

Wannan na zuwa ne bayan sanarwar Gwamnatin Tarayya na raba tirelolin shinkafa ga kowace jiha da ke fadin ƙasar saboda kunci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.