Gwamnati Tayi Damarar Komawa Kotu Cigaba da Shari'a da Mutum 300 da Ake Zargi da Ta'addanci
- Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin komawa kotu kan tuhumar da take yiwa mutane da dama a kasar nan kan ta'addanci
- Hukumomin tsaron kasar sun cafke mutane da dama da ake tuhuma da ta'addanci ko daukar nauyinsa, kuma yanzu za a koma kotu
- Yanzu haka alkalai a manyan kotunan tarayya akalla guda biyar ne za su saurari shari'ar da gwamnati ke yi da wasu mutane 300
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na komawa kotu domin ci gaba da shari'a da a daruruwan mutane da ake zargi da ta'addanci ko alaka da shi a kasar nan.
Gwamnatin za ta yi shari'a da mutane 300 da ake zargin su nada hannu cikin tashe-tashen hankula a Najeriya domin tabbatar da adalci ga jama'a.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa jami'an tsaro sun cafke mutanen daga bangarorin kasar nan da dama bisa zargin hannu dumu-dumu cikin ta'addanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alkalai 5 za su saurari shari'ar ta'addanci
Alkalai guda biyar ne a manyan kotunan tarayya da ke zamansu a wurare daban-daban za su saurari karar da gwamnati ta shigar a kan wadanda ta ke zargi da ta'addanci.
Jaridar The Cable ta wallafa cewa kafin yanzu, sama da kundin bayanan mutane 800 da ake zargi da ta'addanci aka bincike gabanin shari'ar.
A shari'ar da aka yi da wadanda ake zargi da ta'addanci a tsakanin shekarar 2017 da 2018, an yi nasarar daure miyagu 163, an kori kararraki 882, sannan ba a samu mutum biyar da laifi ba.
"A daina alakanta ni da ta'addanci," Matawalle
A baya mun kawo labarin yadda karamin ministan tsaro, kuma tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ja kunnen masu alakanta shi da ta'addanci.
Bello Matawalle ya ce sai da jami'an tsaro su ka kammala bincike a kan shi tsaf kafin gwamnati ta nada shi mukamin karamin ministan tsaron Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng