"Tilas Kowa Ya Biya Direbobi, Sauran Ma'aikatansa Akalla N70,000," Shugaban Majalisa
- Majalisar dattawa ta bayyana cewa tilas ne kowanne mai daukar aiki a Najeriya ya biya mafi karancin albashi ga ma'aikatansa
- Wannan na zuwa bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu a kan dokar mafi karancin albashi a wata
- Saboda haka, shugaban majalisar ya ce N70,000 aka amince kowanne mai daukar aiki ya bayar ga wadanda ya dauka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana cewa sabon mafi karancin albashin N70,000 ya shafi bangarorin gwamnati da masu zaman kansu.
A karin bayanin da Sanata Akpabio ya yi yayin zaman majalisa a ranar Talata, ya bayyana cewa albashin N70,000 ya shafi har masu wanke-wanke, shara da sauran ayyukan gida.
Jaridar Punch ta wallafa cewa sun yi murna da samar da sabon tsarin mafi karancin albashi, kuma su na sa ran kowanne mazaunin kasar nan da zau dauki wani aiki ya biya N70,000.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Karin albashi ya shafi kowa," Shugaban majalisa
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya taya kungiyar kwadago murnar nasara a kan gwamnatin tarayya wajen fitar da sabon tsarin mafi karancin albashi.
Ya kara da cewa nasara ce babba da ya ake sa ran dukkanin masu ikon daukar aiki a kasar nan za su aiwatar, Jaridar Independent ta wallafa.
Karin bayani kan albashin ma'aikata
"Idan kai tela ne ka dauki karin masu dinki, ba za ka biya su kasa da N70,000 ba. Idan ke uwa ce mai karamin jariri, kuma ki na bukatar daukar mai kula da danki, ba za ki biya abin da ya yi kasa da mafi karancin albashi ba. Mafi karancin albashi ne, ya shafi kowa.
- Shugaban majalisa, Sanata Godswill Akpabio
Majalisa ta amince da mafi karancin albashi
A wani labarin kuma kun ji cewa majalisar kasar nan ta amince da kudurin mafi karancin albashi da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya aika mata.
Wannan na nufin an samu karin mafi karancin albashin ma'aikata daga N30,000 zuwa N70,000 bayan kwaskwarima ga dokar mafi karancin albashin 2019.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng