Shugaban NNPP Ya 'Lakadawa' Wata Mata Dukan Tsiya a Kano, An Samu Bayanai
- Wata mata a jihar Kano ta fito ta zargi shugaban jam'iyyar NNPP na ƙaramar hukumar Dawakin Tofa da yi mata dukan tsiya
- Hajiya Bilkisu ta ce ta je karɓar tallafi ne a gidan gwamnatin jihar lokacin da shugaban na NNPP ya huce fushinsa a kanta
- Matar ta bayyana cewa sakamakon dukan da ya yi mata, ta samu raunuka sosai a ƙirji, baya, wuya da kuma fuska
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Ana zargin shugaban jam'iyyar NNPP na ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano da laifin lakaɗawa wata mata dukan tsiya a gidan gwamnatin jihar.
Wata mata mai suna Hajiya Bilkisu ce ta yi wannan zargin kan Malam Baban Iya na cewa ya yi mata dukan tsiya a gidan gwamnatin Kano.
Wane zargi aka yi wa shugaban NNPP?
Matar ta ce lamarin ya auku ne a lokacin da take kan layi domin karɓar N50,000 a ƙarƙashin shirin tallafawa mata na wata-wata da gwamnatin jihar ta ɓullo da shi, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hajiya Bilkisu da ta yi magana daga kan gadon asibiti, ta yi zargin cewa, sakamakon dukan da ya yi mata, ta samu munanan raunuka a fuska, ƙirji, baya da kuma wuyanta.
Ta bayyana cewa lamarin ya fara ne bayan an cire sunanta daga jerin waɗanda za su ci gajiyar tallafin.
Yadda shugaban NNPP ya jibgi mata
Ta yi zargin cewa ɗaya daga cikin jami’an ne ya kira shugaban na NNPP ta wayar tarho, daga nan kawai sai ga shi ya bayyana a wajen, sannan ya rufar mata da duka ta ko ina.
Hajiya Bilkisu ta yi kira ga ƴan sanda da su shiga cikin lamarin da nufin ganin an yi mata adalci.
Da gaske shugaban NNPP ya doki mata?
Da aka tuntuɓi Malam Baban Iya ta wayar tarho, ya amince cewa ya bugi matar, amma ya ce hakan ya faru ne saboda wani abu na daban.
Sai dai, bai bayyana abin da ta yi masa ba wanda ya sanya ya ɗauki wannan matakin a kanta.
Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?
Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.
Kakakin ya bayyana cewa sai ya je ofis zai bincika ya ga takamaiman abin da ya faru.
Jam'iyyar NNPP ta gargaɗi Bola Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar NNPP a jihar Kano, Hashimu Dungurawa ya yi tsokaci kan rigimar sarautar jihar da ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa.
Dungurawa ya ce rashin tsoma bakin Bola Tinubu a rigimar masarautar Kano zai iya kawo masa cikas a babban zaɓen 2027 da ake tunkara nan da wasu ƴan shekaru.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng