Wasu Matasan Arewa Sun Fadi Sharuda 3 Kafin Janye Zanga Zangar da Aka Shirya
- Yayin da ake ta samun wasu kungiyoyi a kasar nan su na janye aniyar shiga zanga-zanga, wasu matasan jihar Kano sun ce babu fashi
- Kungiyar kare hakkin dan Adam da yaki da rashin adalci ta shaidawa Legit cewa har yanzu ta na kan bakarta, amma za ta iya janyewa
- Shugaban kungiyar, Kwamred Umar Shu'aibu Umar ya ce da zarar shugaban kasa Bola Tinubu ya tabbatar da karya farashin fetur, sun janye
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Kungiyar kare hakkin dan Adam da yaki da rashin adalci ta ce batun zanga-zanga babu fashi matukar gwamnati ba ta dauki gamsassun matakai ba. Wannan na zuwa a lokacin da wasu kungiyoyin matasa a Arewa da Kudancin kasar nan ke ta janyewa daga tsunduma zanga-zanga kan halin da kasa ke ciki.
Legit ta zauna da masu niyyar zanga-zanga
A tattaunawar shugaban kungiyar, Kwamred Umar Ibrahim Umar da Legit, ya ce su kam su na kan bakarsu na shiga zanga-zanga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A zaman shugaban kungiyar, Kwamred Umar Ibrahim Umar da Legit, ya ce su kam su na kan bakarsu na shiga zanga-zangar lumana.
Matasa za su iya fasa zanga-zanga
Daya daga cikin kungiyoyin matasa da ke jagorantar shirya zanga-zangar gama gari a Kano ta ce za ta iya fasa aniyarta bisa sharadi.
Shugaban kungiyar, Kwamred Umar Ibrahim Umar ya ce daya daga cikin sharudan shi ne gwamnati ta dawo da farashin fetur kasa da N300.
Sauran sharadun da ya bayyana sun hada da samun saukin farashin kayan abinci da raguwar matsalolin da ya sa aka shirya zanga-zanga tun da fari.
"Dole ta sa za ayi zanga-zanga" Matasa
Shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam da yaki da rashin adalci ta ce ba a son ran matasan kasar nan za a gudanar da zanga-zanga ba.
Kwamred Umar ya ce amma zanga-zanga ce kaɗai hanyar da gwamnati za ta saurari koken 'yan Najeriya. Ya ce sun kammala shirin kare zanga-zangar lumana da su ka shirya daga bata-garin jama'a daga ranar 1-15 Agusta, 2024.
Zanga-zanga: Shugaba Tinubu ya roki matasa
A baya mun ruwaito cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya roki 'yan kasar nan da su ajiye aniyarsu ta shiga zanga-zangar gama gari kan matsin rayuwa. Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris ne ya mika sakon Tinubu, inda ya ce ya ji koken 'yan kasar nan, kuma za a dauki mataki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng