Matawalle ya Samu Kariya Kan Zargin Ta'addanci, 'Dan Siyasa ya Kira Turji Rikakken Maƙaryaci

Matawalle ya Samu Kariya Kan Zargin Ta'addanci, 'Dan Siyasa ya Kira Turji Rikakken Maƙaryaci

  • Kungiyar masu kishin kasa da rajin kawo ci gaba ta kawo wa karamim ministan tsaro, Bello Matawalle dauki a kan zargin ta'addanci
  • Babban sakataren kungiyar, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi ya bayyana cewa babu kamshin gaskiya a kan zargin Matawalle na goyon bayan ta'addanci
  • Wannan na zuwa a matsayin martani kan kasungurmin dan ta'adda, Bello Turji da ya fito ya na zargin Matawalle da marawa ta'addanci baya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Tsohon Sakataren jam'iyyar APGA na kasa, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi ya kawo wa karamin ministan tsaro, Bello Matawalle dauki kan zargin alaka da ta'addanci.

Kara karanta wannan

Shugaban bankin cigaban Afrika, Akinwumi Adesina ya fadi illar 'bita da kulli' ga matatar dangote

Dr. Sani Shinkafi ya ce tsagwaron karya ne zargin da Kachalla Bello Turji ya yi kan Bello Matawalle na goyon bayan ta'addancin lokacin ya na gwamnan Zamfara.

Dr Bello Matawalle
Wata kungiya ta kasa ta karyata alaka tsakanin karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da ta'addanci Hoto: Dr Bello Matawalle
Asali: Facebook

Vanguard News ta wallafa cewa Dr. Sani Abdullahi Shinkafi, wanda shi ne babban daraktan kungiyar masu kishin kasa ya ce zarge-zargen Turji ba su da tushe ballantana makama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matawalle: "Bello Turji makaryaci ne," Shinkafi

Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ya bayyana cewa dan ta'adda Bello Turji makaryaci ne, kuma ya yi sharrin ne domin kawar da hankali daga mummunan aikinsa.

Dakta Shinkafa ya ce babu wani mai hankali da zai aminta da kalaman dan ta'adda irin Turji, Jaridar Leadership ta wallafa wannan.

Turji: "Matawalle ba zai girgiza ba," Shinkafi

Ya ce kalaman nasa na kokarin bata sunan Bello Matawalle a daidai lokacin da jami'an tsaro ke luguden wuta a kan 'yan ta'adda a kasar nan.

Kara karanta wannan

Kotu ta amince 'danuwan Yahaya Bello da ake zargi da badakalar N3bn ya tafi kasar waje

Babban daraktan ya jaddada cewa babu abin da zai firgita Matawalle ko kawar masa da hankali kan kokarin gwamnatin Bola Tinubu na kawar da 'yan ta'adda.

Turji ya zargi Matawalle da ta'addanci

A baya mun kawo labarin yadda fitinannen dan ta'adda, Bello Turji ya bayyana dalilin habakar rashin tsaro da sauran ayyukan ta'addanci a wani sashe na yankin Arewa maso yamma. Turji, wanda ya gallabi jama'a da garkuwa da mutane da kashe-kashe ya zargi karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da hannu dumu-dumu cikin goyon bayan 'yan ta'adda da ta'addanci a Zamfara

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.