Ana Zargin An Rabawa 'Yan Majalisa Cin Hancin N400m Domin Amincewa da Bukatar Tinubu

Ana Zargin An Rabawa 'Yan Majalisa Cin Hancin N400m Domin Amincewa da Bukatar Tinubu

  • Yayin da ake kukan rashin abin hannu a Najeriya, an yi zargin cewa gwamnatin tarayya ta fitar da makudan kudi domin rabawa ga majalisa
  • Wani mawallafin jarida, Jafar Jafar ya ce an ba wa kowanne Sanata N400m domin a gaggauta amincewa da kudurin mafi karancin albashi
  • Tuni 'yan Najeriya su ka fara martani, inda su ka ce wannan na daga manyan dalilan da za su tsunduma zanga-zanga da ake shirin yi daga 1-15 Agusta, 2024

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Yayin da majalisar kasar nan ta gaggauta amincewa da kudurin mafi karancin albashi, an bankado dalilin saurin wucewar kudurin.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya miƙa kudirin sabon mafi ƙarancin albashi ga majalisa, bayanai sun fito

An zargi gwamnatin tarayya da bayar da cin hanci mai nauyi ga 'yan majalisar domin amincewa da kudurin mafi karancin albashi a cikin awanni.

Bola Tinubu
Kudurin albashi: An zargi Shugaba Tinubu da mika na goro ga majalisa Hoto: Bola Tinubu/Nigerian Senate
Asali: Facebook

Mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jafar Jafar ta wallafa zargin a shafinsa na X cewa an ba wa kowane Sanata kyautar Naira Miliyan 400.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya 'rabawa' 'yan majalisar wakilai N200m

'Dan jaridar ya yi zargin cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayar da na goro ga 'yan majalisar wakilai.

A zargin da ya yi, ya ce kowane wakili ya samu N200m domin gaggauta tabbatar da dokar mafi karancin albashi na N70, 000 ga ma'aikatan Najeriya.

Martanin jama'a kan zargin ba 'yan majalisa kudi

Wasu masu amfani da dandalin X sun fara martani kan yadda aka yi zargin shugaba Tinubu ya yi 'kyauta' ga 'yan majalisa saboda kudurin mafi karancin albashi.

Kara karanta wannan

Za a sha jar miya, Tinubu ya fadi yadda zai kashewa 'Yan Najeriya N6.2tn a kasa da wata 6

@AbbaM_Abiyos ya ce;

"Karin dalilin da za mu gudanar da zanga-zanga."

@Ibrahiimsmd ya ce;

"Karin kasafin kudi na 'yan majalisa ne ba 'yan Najeriya ba."

Majalisa ta amince da kudirin albashi

A baya mun kawo labarin yadda 'yan majalisar kasar nan su ka gaggauta amincewa da kudurin dokar mafi karancin albashi da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya aika masu da shi. An amince da dokar bayan ya gaggauta wuce karatu na daya da na biyu da na uku a zaman majalisar da ya gudana a ranar Talata, inda a yanzu kasar nan za ta rika biyan N70, 000 mafi karancin albashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.