An Samu Matsala a Zaman Kotu Kan Shari’ar da Kwankwaso Ya Shigar da Hukumar EFCC

An Samu Matsala a Zaman Kotu Kan Shari’ar da Kwankwaso Ya Shigar da Hukumar EFCC

  • Babbar Kotun jihar a Kano ta yi zama kan shari'ar da Sanata Rabiu Kwankwaso ke karar hukumar EFCC kan hakkinsu na 'yan kasa
  • Kwankwaso ya shigar da korafi tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar NNPP yayin da hukumar ke zarginsa da bakadalar makudan kudi
  • Alkalin kotun, Mai Shari'a, Yusuf Ubale ya dage ci gaba da sauraran shari'ar zuwa ranar 24 ga watan Oktoban shekarar 2024

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - An samu matsala a shari'ar da Sanata Rabiu Kwankwaso ya shigar da kara kan take hakkinsu na 'yan kasa.

An samu matsala bayan hukumar EFCC ta gaza shiryawa kan karar da Sanatan ya shigar a gaban Babbar Kotun jihar Kano.

Kara karanta wannan

Kotu ta amince 'danuwan Yahaya Bello da ake zargi da badakalar N3bn ya tafi kasar waje

An samu tasgaro a shari'ar Kwankwaso da hukumar EFCC
Kotu ta dage sauraran karar da Kwankwaso ya shigar da EFCC zuwa watan Oktoban 2024. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Economic and Financial Crimes Commission.
Asali: UGC

Kotu ta zauna a shari'ar Kwankwaso - EFCC

Kwankwaso ya shigar da korafin ne da wasu mutane bakwai da suka hada da Dakta Ajuji Ahmed da Ahmed Balewa a cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada da Dipo Olayanku da Cif Clement Anele da Lady Folashade Aliu da kuma jigon jam'iyyar NNPP, Buba Galadima.

Yayin zaman kotun a yau Talata 23 ga watan Yulin 2024, lauyan masu kara, Barista Robert Hon ya fadawa kotun cewa sun shirya tsaf domin sauraran shari'ar, Daily Trust ta tattaro.

Hon ya roki kotun da ta yi watsi da bukatar wadanda ake zargi na neman dage ci gaba da shari'ar saboda rashin shiri.

Kwankwaso: EFCC ta roki kotu karin lokaci

Har ila yau, lauyan wadanda ake zargi, Idris Ibrahim Haruna ya bukaci kotun ta dage sauraran shari'ar domin ba su damar shiryawa.

Kara karanta wannan

Ana saura kwana 10 ayi zanga zanga, Tinubu ya dawo Najeriya bayan kammala taron AU

Daga bisani alkalin kotun, Mai Shari'a, Yusuf Ubale Muhammad ya dage ci gaba sauraran karar zuwa ranar 24 ga watan Oktoban 2024.

Wannan na zuwa ne bayan kotu ta dakatar da EFCC daga kamawa da cin zarafi ko barazana ga Kwankwaso da mutanen bakwai.

Kwankwaso ya maka EFCC a kotu

Kun ji cewa babbar kotun Kano za ta fara zaman sauraron ƙorafin da Rabiu Musa Kwankwaso da wasu mutum bakwai suka shigar da EFCC.

Jagoran NNPP da sauran mutanen su bakwai sun maka hukumar yaƙi da rashawa EFCC a gaban kotun ne kan abin da ya shafi tauye haƙƙinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.