Majalisa Ta Dauki Mataki Kan Kudirin Sabon Mafi Karancin Albashi da Tinubu Ya Mika
- Majalisar dattawan Najeriya ta amince da ƙudirin dokar mafi ƙarancin albashi na shekarar 2019 (wanda aka yi wa kwaskwarima)
- Amincewa da ƙudirin dokar na zuwa ne bayan ya tsallake karatu na ɗaya, na biyu da na uku a yayin zaman majalisar na ranar Talata
- Shugaban ƙasa Bola Tinubu ne ya miƙa ƙudirin gaban majalisar domin ƙara mafi ƙarancin albashin ma'aikata daga N30,000 zuwa N70,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta yi gaggawar amincewa da ƙudirin dokar mafi ƙarancin albashi na ƙasa na shekarar 2019 (wanda aka yiwa kwaskwarima).
Majalisar ta amince da ƙudirin dokar ne a yayin zamanta na ranar Talata, 23 ga watan Yulin 2024.
Majalisa ta amince da ƙudirin albashi
Tashar Channels tv ta ce ƙudirin dokar ya samu karatu na ɗaya da na biyu da na uku tare da amincewa da shi ƴan mintoci kaɗan bayan an gabatar da shi a gaban majalisar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar ta amince da kuɗirin ne bayan ya tsallake karatu na uku inda duka sanatocin suka kaɗa ƙuri'ar amincewa da shi, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
Tinubu ya miƙa ƙudiri gaban majalisa
A ranar Talata, shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya miƙa ƙudirin ga majalisar domin neman yin la'akari a kansa tare amince da shi.
Shugaban ƙasan ya rubuta wasiƙa ga majalisar dattawa da majalisar wakilai inda ya buƙaci duba kan ƙudirin da zai yi kwaskwarima ga dokar mafi ƙarancin albashi ta 2019.
Wannan zai ba da dama domin ƙara mafi karancin albashin daga N30,000 zuwa N70,000.
Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci ƴan majalisar da su rage lokacin yin waiwaye kan dokar daga shekara biyar zuwa shekara uku.
Miƙa ƙudirin a gaban majalisar na zuwa ne biyo bayan matsayar da aka cimmawa tsakanin Shugaba Tinubu da ƴan kwadago kan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Gwamna Adeleke zai biya albashin N70,000
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi magana kan batun biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 duk wata.
Gwamna Ademola Adeleke a ranar Juma'a, 19 ga watan Julin 2024 ya yi alƙawarin cewa zai biya ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashin na N70,000.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng