Shugaban Bankin Cigaban Afrika, Akinwumi Adesina Ya Fadi Illar 'Bita da Kulli' ga Matatar Dangote

Shugaban Bankin Cigaban Afrika, Akinwumi Adesina Ya Fadi Illar 'Bita da Kulli' ga Matatar Dangote

  • Shugaban bankin cigaban Afrika, Dr. Akinwumi Adesina ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta jawo wa kasar nan matsala
  • Shugaban na martani ne kan takun saka da ya shiga tsakanin Attajirin Afrika, Aliko Dangote da wasu kusoshin gwamnatin tarayya
  • Mista Adesina na ganin irin wannan sa'insa ka iya ba wa masu kokarin sanya hannun jari a Najeriya tsoro, kuma su fasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Shugaban bankin cigaban Afrika (AfDB), Akinwumi Adesina ya ce fadi-in-fada da ke wakana tsakanin Attajirin nahiyar nan, Aliko Dangote da gwamnatin tarayya babbar illa ce.

Kara karanta wannan

An fusata Dangote, mai kudin Afrika ya fara tona asirin manyan jami'an NNPCL

Dakta Adesina ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ce za ta yi asara matakur aka ci gaba da yiwa Dangote da matatar mansa 'bita-da-kulli.'

Dangote
Dangote: Shugaban bankin Afrika, Akinwumi Adesina ya ce Najeriya ce za ta yi asara Hoto: Earnest Ankomah/Florian Gaertner
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa shugaban bankin AfDB ya kuma yi watsi da batun cewa Aliko Dangote na kokarin kankane kasuwar man fetur a kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A 'yan kwanakin nan dai an samu baraka tsakanin gwamnatin tarayya da Dangote inda wasu jami'ai su ka rika zargin matatar Dangote ta Legas da fitar da mai mara kyau.

"Rikici da Dangote zai kori 'yan kasuwa," Adesina

Shugaban bankin cigaban Afrika, Dakta Akinwumi Adesina ya bayyana cewa takun saka da ake samu tsakanin gwamnati da Aliko Dangote barazana ce ga masu son zuba jari a kasar nan.

Dakta Adesina ya yi fatali da zargin da gwamnatin tarayya ta yi na cewa Dangote na son mamaye kasuwar fetur, Jaridar Vanguard ta wallafa.

Kara karanta wannan

Bayan an karrama shi, Farfesa Wole Soyinka ya fadi abin da zai yi a kan gwamnatin Tinubu

Shugaban ya kara da cewa kasancewar an saba shigo da man fetur daga kasashen ketare ya sa wasu a kasar nan ke ganin hakan shi ne dai-dai.

Dangote ya ce ba shi da hadama

A baya mun ruwaito cewa shugaban rukunin kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya bayyana cewa ba shi da hadama, sabanin yadda wasu su ke zarginsa.

Wasu jami'an gwamnati sun yi zargin cewa Aliko Dangote na son a bar shi shi kadai ya rika juya kasuwar man fetur a kasar nan yadda ya ga dama, lamarin da Dangote ya ce ba gaskiya ba ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.