Shugaban NNPCL, Kyari Ya Yi Zazzafan Martani ga Dangote Kan Kalamansa

Shugaban NNPCL, Kyari Ya Yi Zazzafan Martani ga Dangote Kan Kalamansa

  • Yayin da attajiri Aliko Dangote ya yi zargin masa zagon kasa, shugaban NNPCL, Mele Kyari ya mayar masa da martani
  • Kyari ya ce ba shi da wani kamfanin mai a kasar Malta kamar yadda Dangote ya yi zargi inda ya ce hakan ba gaskiya ba ne
  • Shugaban na NNPCL ya ce ba shi da masaniya a cikin ma'aikatan kamfaninsa wani na da alaka da irin wannan zargi da ake yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari ya mayar da martani ga Alhaji Aliko Dangote kan zarge-zargensa.

Mele Kyari ya musanta zargin Dangote na cewa yana da kamfanin mai da yake gudanarwa a kasar Malta da ke yankin Turai.

Kara karanta wannan

An fusata Dangote, mai kudin Afrika ya fara tona asirin manyan jami'an NNPCL

Kamfanin NNPCL ya mayar da martani ga Dangote kan maganganunsa
Shugaban NNPCL, Mele Kyari ya musanta dukan maganganun Dangote game da masa zagon kasa. Hoto: NNPC Limited, Dangote Foundation.
Asali: Facebook

Kamfanin NNPCL ya musanta zargin Dangote

Shugaban kamfanin ya bayyana haka ne a yau Talata 23 ga watan Yulin 2024 a Abuja, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kyari ya ce ba shi da masaniyar cewa wani daga cikin ma'aikatan NNPCL yana gudanar da kamfanin tace mai a kasar Malta, cewar Punch.

Kyari ya ce idan har akwai wanda ya ke da hannu a lamarin ya bukaci bayyana sunansa saboda gwamnati ta dauki mataki kansa.

NNPCL: Kyari ya yi martani ga Dangote

"Na yi ta samun korafi da tambayoyi kan ikirarin Aliko Dangote game da cewa wasu ma'aikatan NNPCL suna da kamfanin mai a Malta domin kawo cikas ga masu samar da mai a gida."
"Domin fayyace zargi kan wannan lamari, ba ni da kamfani ko gudanar da kamfani a wata kasa idan ban da dan karamin kamfanin harkar noma ba."

Kara karanta wannan

Kotu ta amince 'danuwan Yahaya Bello da ake zargi da badakalar N3bn ya tafi kasar waje

"Daga ni har sauran ma'aikatan NNPCL babu wani da ke gudanar da wannan kamfanin da ake magana a Malta ko wasu kasashe."

- Mele Kyari

Dangote zai siyar da matatar mansa

A wani labarin, kun ji cewa attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika, Aliko Dangote ya ce a shirye yake ya sayar da matatar mansa.

Dangote ya ce ya shirya sayar da matatar man fetur ɗin ta biliyoyin daloli ga kamfanin mai na NNPCL idan suna bukatar hakan.

Attajirin ya yi magana ne a yayin da dangantaka ta fara yin tsami tsakaninsa da hukumomi a ɓangaren makamashi na Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.