Shugaban Majalisa, Akpabio Ya Shiga Matsala Bayan Yin Gatsali ga Sanatar PDP

Shugaban Majalisa, Akpabio Ya Shiga Matsala Bayan Yin Gatsali ga Sanatar PDP

  • Kungiya mai fafutukar kare hakkin mata (VIEW) ta caccaki shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio
  • Kungiyar VIEW ta caccaki Godswill Akpabio ne bayan magana da ya yiwa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a zaman majalisa
  • Kungiyar ta zargi Akpabio da muzgunawa wata Sanata mace mako daya kafin ya yi magana a kan Natasha Akpoti-Uduaghan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya fara shan suka bayan zargin ya dakatar da mata Sanatoci daga magana.

Wata kungiya mai fafutukar kare hakkin mata ta yi martani mai zafi ga Akpabio inda ga bakaci a dauki mataki a kansa.

Sanata Akpabio
Shugaban Majalisa ya sha suka kan dakatar da mata Sanatoci daga magana. Hoto: Nigerian Senate
Asali: Twitter

Jaridar the Cable ta ruwaito cewa kungiyar VIEW ta zargi da Sanata Akpabio da nuna wariyar jinsi ga mata a majalisar.

Kara karanta wannan

Magana ta kare, sanatoci sun raba gardama kan 'shirin tsige' shugaban Majalisar Dattawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akpabio: Abin da ya faru a majalisar dattawa

Shugaban majalisa Godswill Akpabio ya dakatar da Sanata Natasha Akpoti daga magana inda ya ce mata majalisar ba gidan gala bane saboda ta yi magana ba tare da izini ba.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Akpabio ya taba buƙatar Sanata Sanata Ireti Kingibe ta yi shiru yayin da take shigar da korafi a majalisar.

Illar dakatar da mata daga magana a Majalisa

Kungiyar VIEW ta bayyana cewa dakatar da mata daga magana zai rage tabbatar da samun mulki na gari a Najeriya.

VIEW ta ce akwai bukata mai tsanani na ganin an samu mata na magana a harkar gwamnati domin suma wakilai ne na al'umma.

VIEW ta bukaci a dauki mataki kan Akpabio

Kungiyar VIEW ta ce ya kamata a dauki mataki a kan Godswill Akpabio domin dorewar dimokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

Da gaske alaka ta yi tsami tsakanin Majalisar Tarayya da Tinubu? an samu bayanai

Cikin matan da suka rattaba hannu a kan takardar da VIEW ta sake akwai Maryam Lemu, Kadaria Ahmed, Aisha Waziri, Mairo Mandara da sauransu.

Sanata Akpabio ya zargi Godwin Emefiele

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya yi jawabi kan matsalar tattalin arziki da ta addabi kasar nan.

Sanata Akpabio ya ce dukkan matsalolin da ake ciki yanzu suna da nasaba da irin tsare-tsaren da Godwin Emefiele ya kawo a lokacin Muhammadu Buhari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng