An Fusata Dangote, Mai Kudin Afrika Ya Fara Tona Asirin Manyan Jami'an NNPCL

An Fusata Dangote, Mai Kudin Afrika Ya Fara Tona Asirin Manyan Jami'an NNPCL

  • Mutumin da ya fi kowa kudi a Afrika, Aliko Dangote ya zargi wasu daga cikin ma'aikatan kamfanin mai na kasa da mallakar karamin wajen gyara mai
  • Alhaji Aliko Dangote ya ce haka kuma akwai wasu daga cikin masu kasuwancin mai da su ka mallaki irin wannan wurin gyaran fetur a Malta
  • Alhaji Dangote ya kara jaddada ingancin man da matatarsa da ke Legas ke fitar wa, inda ya ce ya fi wanda ake shigo wa da shi inganci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya ce wasu daga cikin jami'an kamfanin man fetur na kasa (NNCPL) da wasu daga cikin masu kasuwancin mai sun mallaki karamin wurin tace mai a Malta.

Kara karanta wannan

Shugaban bankin cigaban Afrika, Akinwumi Adesina ya fadi illar 'bita da kulli' ga matatar dangote

Alhaji Aliko Dangote ya ce sun san wuraren da kananan wurin tace danyen man fetur ya ke a Malta, a dai-dai lokacin da ake zarginsa da fitar da mai mara inganci.

Dangote
Aliko Dangote ya zargi wasu jami'an NNPCL da mallakar wurin gyara mai a ketare Hoto: Earnest Ankomah
Asali: Getty Images

Channels Television ta wallafa cewa Aliko Dangote ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabancin majalisa karkashin kakakinta, Tajuddeen Abbas da mataimakinsa, Benjamin Kalu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote ya nanata kyawun fetur din matatarsa

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika ya ce fetur din da matatarsa ta Legas ke samar wa ya fi wanda ake shigo da shi kasar nan kyau.

Dangote ya ce wasu daga cikin matsalolin da ababen hawa ke samu a kasar nan sun samo asali ne daga rashin ingancin man da ake zuba wa.

Ya shawarci shugabancin majalisar kasar nan ta kafa kwamiti mai zaman kansa domin binciken ingancin fetur din da ake sayar wa 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPCL, Kyari ya yi zazzafan martani ga Dangote kan kalamansa

Dangote ya yiwa NNPCL tayin matatar fetur

A wani labarin kun ji cewa a shirya ya ke da sayar wa kamfanin mai na kasa (NNPCL) da matatar mansa ta biliyoyin daloli da aka shafe shekaru ana gina wa.

Alhaji Aliko Dangote na wannan batu ne a matsayin martani kan hukumar NMDPRA da ta ce man dizal din da kamfaninsa ke samar wa ba shi da inganci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.