Shugaba Tinubu Ya Mika Kudirin Sabon Mafi Karancin Albashi ga Majalisa, Bayanai Sun Fito
- Bola Ahmed Tinubu ya aika kudirin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata na N70,000 ga majalisar wakilai ranar Talata, 23 ga watan Yuli
- Shugaban ƙasar ya buƙaci ƴan majalisar su gaggauta amincewa da kudirin sabon albashin domin aiwatar da shi a kan lokaci
- Haka nan Tinubu ya bukaci majalisar ta yi wa kundin dokokin rundunar ƴan sandan Najeriya garambawul kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kudirin sabon mafi karancin albashi ga majalisar wakilai domin tantancewa tare da amincewa da shi.
Ana sa ran kudirin dokar zai zaratar da mafi karancin albashi na N70,000 wanda aka amince da shi kwanan nan ya zama doka a Najeriya.
Shugaba Bola Tinubu ya kai kudirin albashi
The Nation ta ce Idan baku manta ba gwamnatin tarayya, kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin kwadago sun cimma matsaya kan N70,000 ranar Alhamis da ta wuce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasikar shugaban wadda aka karanta a zauren majalisar yau Talata, ta ƙunshi sabon albashi mafi karanci na N70,000 da kuma tsarin aiwatar da shi, Channels tv ta rahoto.
Bola Tinubu ya roƙi ‘yan majalisar su gaggauta amincewa da kudurin dokar domin fara aiwatar da shi a kan lokaci kuma ma'aikatan gwamnati su fara cin gajiya.
Tinubu ya nemi gyara dokar ƴan sanda
Bayan haka Shugaban ya miƙa bukatar yiwa dokar rundunar ƴan sanda garambawul ga majalisar wakilai ta ƙasa.
Ya roƙi ‘yan majalisar su yi wa dokar ƴan sanda garambawul kamar yadda sashe na 58 na kundin tsarin mulkin kasa na 1999 ya tanada.
Abin da shugaban kasar ya buƙaci gyara shi ne dokokin rundunar ‘yan sanda dangane da nadi da kuma wa’adin ofishin Sufeto Janar na ‘yan sanda.
Ƴan aiki za su sha romon karin albashi
A wani labarin kuma Majalisar dattawa tare da kungiyar NCWS sun bukaci a sanya ƴan aikin gida a tsarin sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Kwamitin kwadago da samar da ayyukan yi na majalisar dattawa ya ce ya kamata ƴan aiki su amfana da sabon albashi mafi karanci na ƙasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng