Yusuf Gagdi: Abubuwan Sani Dangane da Dan Majalisar da Ya Siyawa 'Yarsa Motar Kusan 100m

Yusuf Gagdi: Abubuwan Sani Dangane da Dan Majalisar da Ya Siyawa 'Yarsa Motar Kusan 100m

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Yusuf Adamu Gagdi shi ne ɗan majalisar da ke wakiltar Pankshin/Kanam/Kanke a majalisar wakilai ta Najeriya a birnin tarayya Abuja.

A cikin ƴan kwanakin nan labarinsa ya karaɗe shafukan sada zumunta bayan ya yiwa ɗiyarsa kyautar dalleliyar mota domin taya ta murnar kammala karatun sakandire da ta yi.

Abubuwan sani dangane da Yusuf Adamu Gadgi
Yusuf Gagdi na wakiltar Pankshin/Kanam/Kanke a majalisar wakilai Hoto: @HouseNGR, @YusufAdamuGagdi
Asali: Twitter

Abubuwan sani dangane da Yusuf Gagdi

Legit Hausa ta zauna, ta tattaro wasu abubuwan da ya kamata ku sani dangane da ɗan majalisar wanda ya fito daga jihar Plateau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Haihuwar Yusuf Gagdi

An haifi Yusuf Adamu Gagdi ne ranar, 5 ga watan Nuwamban 1985 a ƙauyen Gum-Gadgi da ke gundumar Gagdi a ƙaramar hukunar Kanam ta jihar Plateau.

Kara karanta wannan

Matasa na shirin yin zanga zanga, ɗan majalisar tarayya ya sauya sheƙa zuwa APC

2. Karatu

Ya yi karatunsa na firamare a ƙauyensu na Gum-Gagdi sannan ya kammala karatunsa na sakandire a makarantar sakandire ta GSS Dengi a shekarar 1999.

Ya samu kwalin NCE a shekara 2004 daga kwalejin FCE Pankshin. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Jos a fannin tattalin arziƙi, yana da kwalin PGD da digirin digir a fannin warware rikice-rikice.

Ya yi digirin digir-gir a jami'ar jihar Nasarawa da ke Keffi.

3. Aiki

Yusuf Adamu Gagdi ya fara aiki ne a matsayin malamin makaranta a makarantar sakandire ta GSS Anguwan Rogo.

Daga baya an tura shi zuwa ofishin shugaban ma'aikatan jihar, inda ya yi aiki a ƙarƙashin marigayi Godfrey Mamzhi a matsayin mataimakinsa na musamman.

4. Siyasar Yusuf Gagdi

Yusuf Adamu Gagdi ya wakilci mazaɓar Kantana a majalisar dokokin jihar Plateau, inda ya riƙe muƙamin mataimakin kakakin majalisar dokokin.

A shekarar 2019, an zaɓe shi a matsayin ɗan majalisa mai wakiltar Pankshin/Kanam/Kanke a majalisar wakilai a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Rikici ya ɓarke a taron da Aminu Ado ya halarta, an farmaki ɗan majalisar NNPP

Ya kuma sake lashe zaɓensa a zaɓen shekarar 2023, inda ya zama mutum na farko da ya taɓa lashe zaɓe karo na biyu a tarihin mazaɓar.

Ya riƙe muƙamin shugaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin sojin ruwa.

A shekarar 2023, ya yi takarar kujerar kakakin majalisar wakilai, amma ya janye bayan shugaban ƙasa Bola Tinubu ya buƙaci sauran ƴan takara da su yi hakan, saboda akwai wanda jam'iyyar APC take so ya hau kujerar, cewar rahoton Vanguard.

5. Kafa tarihi a majalisa

Yusuf Adamu Ga ya kafa tarihin zama ɗan majalisar wakilai wanda a zuwansa na farko majalisa ya kawo ƙudiri guda shida waɗanda shugaban ƙasa ya rattaɓawa hannu, rahoton jaridar Thisday ya tabbatar.

Yusuf Gagdi ya yi wuff da Laylah Ali Othman

A wani labarin kuma, kun ji cewa shahararriyar ƴar kasuwar nan ta Arewa wacce ta yi fice a bangaren kayan alatu da kawata gida, Laylah Ali Othman ta shiga daga ciki.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa ta yi babbar barna a jihar Arewa, mutum 1,664 sun rasa matsugunni

An daura auren Laylah da angonta, Yusuf Gagdi, wanda ya kasance dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Pankshin/Kanke/Kanam ta jihar Filato a ranar Juma'a, 13 ga watan Oktoban 2023.

Laylah Ali Othman tana da kamfaninta mai suna L and N Interiors’, tana sana’ar buga mujallun zamani, sannan ta kasance yar kare haƙƙin mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng