N70,000: Ƴan Aikin Gida Za Su Sha Romo, Majalisa da Ƙungiyar NCWS Sun Miƙa Bukata
- Majalisar dattawa tare da kungiyar NCWS sun bukaci a sanya ƴan aikin gida a tsarin sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000
- Kwamitin kwadago da samar da ayyukan yi na majalisar dattawa ya ce ya kamata ƴan aiki su amfana da sabon albashi mafi karanci na ƙasa
- Shugaban kwamitin, Sanata Diket Plang ya ce za a kafa hukumar da za tabbatar da an aiwatar da wannan doka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Majalisar Dattawa da Ƙungiyar Mata ta Kasa (NCWS) sun nemi a saka masu aikin gida a cikin tsarin sabon mafi karancin albashi na N70,000.
Hakan na ɗaya daga cikin abubuwan da aka ambata a taron jin ra'ayoyin jama'a wanda kwamitin kwadago da samar da ayyukan yi ya shirya a Abuja.
Yan aiki za su samu karin albashi?
Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, an yi taron jin ra'ayoyin jama'a ne kan kudirin inganta ayyukan ƴan aiki da yi masu rijista a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata mai wakiltar Imo ta Yamma, Osita Izunaso da shugabar NCWS, Geraldeen Etuk ne suka nemi sanya ma'aikatan cikin gida a dokar mafi karancin albashi na kasa.
Ma'aikatan cikin gida sun haɗa da ƴar aiki, direba da sauran masu yiwa mutane hidimi a cikin gida.
Majalisa za ta kawo batun karin albashi
Da yake jawabi, Sanata Izunaso ya ce:
"A matsayin 'dan wannan kwamiti, ina jin cewa wani bangaren da za a sanya a cikin wannan kudiri shi ne sanya ma’aikatan gida walau ‘yar aiki ko kuma masu hidima a dokar mafi karancin albashi na N70,000.”
"Tun da an amince N70,000 ya zama albashin ƙananan ma'aikata mafi ƙaranci, ya kamata ma'aikatan gida su shiga ciki, zamu sa batun a kudirin domin aiwatarwa."
Shugaban kwamitin Sanata Diket Plang ya kuma bayyana cewa za a kafa wata hukuma ta musamman da za ta sa ido da tabbatar da aiwatar da dokar, Arise tv ta tattaro.
Sanata Kalu ya koka kan albashinsu
A wani rahoton kuma Sanata wai wakiltar jihar Anambara, Orji Uzo Kalu ya koka kan yadda ake biyan Sanatoci kudi kadan a matsayin albashi
Bayan haka, Sanata Orji ya bukaci a canza tsarin zaman majalisa yadda zai dace da kudin da ake biyansu a matsayin albashi a kowane wata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng