Ministan Tinubu Ya Tsoma Baki a Rigimar Dangote da NNPC, an Cimma Matsaya
- Ƙaramin ministan albarkatun man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, ya yi sasanci tsakanin Dangote, NMDPRA, NUPRC da NNPCL
- Kamfanonin man sun zargin Dangote da samar da kayayyaki masu ƙaranci inganci, cewa na ƙetare sun fi na matatarsa kyau
- Alhaji Aliko Dangote ya musanta zargin inda yace akwai masu yi masa zagon ƙasa a harkar da ya danƙara biliyoyin Naira ya kafa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ƙaramin ministan albarkatun man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, ya shiga tsakani kan rikicin shugaban rukunin kamfofin Dangote da hukumomin lura da man fetur.
A ranar Litinin a Abuja, Sanata Lokpobiri ya gana da Aliko Dangote tare da shugabannin hukumomin NMDPRA, NUPRC da kuma na kamfanin NNPCL.
Wannan na zuwa ne bayan zarge-zarge da cibiyoyin suka yi ga Dangote shi kuma ya mayar da martani inda yace zagon ƙasa ake yi wa sabuwar matatarsa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dangote yayi zargin zagon-ƙasa
Dangote ya zargi cewa kamfanonin mai da ke Najeriya sun bazama wurin ƙoƙarin ganin bayan matatarsa da ya danƙara a ƙasar nan.
Ya yi ikirarin cewa kamfanonin da gangan suke toshe ƙoƙarin matatarsa wurin sayen ɗanyen mai a cikin gida ta hanyar tada farashi sama da na kasuwar duniya.
Hakan ya sa dole matatarsa ke shigo da danyen man daga ƙasashe masu nisa kamar Amurka, abin da yasa farashin man nasa ke ƙaruwa.
Hukumomin mai sun kalubalanci Dangote
A ɓangaren NMDPRA, sun zargi cewa matatar man Dangote tana samar da kayayyaki marasa inganci idan aka kwatanta su da waɗanda ake shigo da su.
Farouk Ahmed, shugaban NMDPRA ya ce ingancin dizal ɗin da ake samarwa a matatar Dangote daidai yake da 665ppm, wanda ba shi da inganci sosai.
Wannan surutu tsakanin ɓangarorin biyu ya janyo sukar jama'a, inda 'yan Najeriya da dama ke kira ga gwamnatin tarayya da tayi duba da lamarin ko don ƙasar.
Ministan man fetur ya yi sasanci
A wata sanarwa da aka fitar a daren Litinin, mai bada shawara na musamman kan yaɗa labarai ga Lokpobiri, Mista Nneamaka Okafor ya ce:
"Masu ruwa da tsakin sun bayyana godiyarsu ga ministan kan shugabancinsa nagari da kuma yadda ya shiga lamarin cikin hanzari.
"Taron ya mayar da hankali wurin samo maslaha ga halin da ake ciki a matatar mai ta Dangote, inda bangarorin suka yarda za su bada hadin kai domin kawo maslaha.’'
Wasu 'yan Najeriya sun fi ni kudi - Dangote
A wani labari na daban, mun bayyana muku cewa fitaccen attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya ce akwai 'yan Najeriya da suka fi shi kudi.
Ya ce ya janye daga yunkurin saka hannun jari a masana'antar tama, don haka masu kudade a Dubai da wasu ƙasashe su kwaso su zo su gyara ƙasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng