Za a Sha Jar Miya, Tinubu Ya Fadi Yadda Zai Kashewa 'Yan Najeriya N6.2tn a Kasa da Wata 6

Za a Sha Jar Miya, Tinubu Ya Fadi Yadda Zai Kashewa 'Yan Najeriya N6.2tn a Kasa da Wata 6

  • Gwamnatin tarayya ta yi bayani kan yadda za ta kashe kudi sama da Naira triliyan 6 a cikin kasa da watanni shida
  • Ministan kasafin kudin da tsare-tsare, Atiku Abubakar Bagudu ne ya bayyana haka ga yan majalisar wakilan Najeriya
  • Atiku Bagudu ya bayyana dalilan da suka sanya gwamnatin tarayya tura kasafin kudin ga majalisa a wannan lokacin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta fitar da bayani kan yadda za ta kashe makudan kudi har Naira triliyan 6.2.

Rahotanni sun nuna cewa Bola Tinubu ya ware kudin ne domin su zama cikato ga kasafin kudin shekarar 2024.

Kara karanta wannan

Sanata ya ce albashin 'yan majalisa ya yi kadan bayan jin za a fara biyan ma’aikata N70,000

Bola Tinubu
Minista ya bayyana yadda Tinubu zai kashe N6.2tn. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ne ya yi bayani ga yan majalisar wakilai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

N6.2tr: An ware kudin karin albashi

Atiku Abubakar Bagudu ya bayyana cewa Bola Tinubu ya ware kudi kimanin Naira triliyan 3 domin fara biyan ma'aikata sabon albashi.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya da samu yarjejeniya tsakaninta da yan kwadago kan dawo da mafi ƙarancin albashi N70,000.

Wasu ayyukan da Tinubu zai yi

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Atiku Bagudu ya ce wasu ayyukan da za a kashe kudin dominsu an riga a fara su.

Ya ambaci hanyar Sokoto zuwa Badagry da hanyar Legas zuwa Kalaba wacce za ta laƙume Naira biliyan 150.

Za kashe kudi a layin dogo

Har ila yau, Ministan kasafin ya bayyana cewa za a kashe kudi domin aikin layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri.

Kara karanta wannan

N70,000: Kalubale 5 da ke gaban 'yan kwadago da ma'aikata bayan karin albashi

Layin dogon zai ratsa ta garuruwa da dama ciki har da Rivers, Imo, Bauchi, Filato, Nasarawa, Gombe da Yobe da sauran jihohi a Kudu da Arewa.

Tinubu zai yi titi a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kai aikin babbar hanya jihar Katsina da ke Arewa maso yammacin Najeriya.

Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya mika sakon godiya ga shugaba Bola Tinubu kan tunawa da su a wannan lokacin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng