Sako Zuwa Ga Tinubu: NLC Ta Fadi Hanyoyi 2 Na Hana Matasan Najeriya Yin Zanga Zanga

Sako Zuwa Ga Tinubu: NLC Ta Fadi Hanyoyi 2 Na Hana Matasan Najeriya Yin Zanga Zanga

  • Kungiyar NLC ta ce doka ce ta ba 'yan Najeriya gudanar da zanga-zangar lumana kuma gwamnati ba za ta iya hana hakan ba
  • Sai dai kungiyar ta ce zama a kan teburin sulhu tsakanin gwamnatin tarayya da masu shirin zanga-zangar zai fi fa'ida a yanzu
  • Shugaban NLC, Joe Ajaero ya aika muhimmin sako ga Shugaba Bola Tinubu kan yadda za a dakile wannan zanga-zangar gaba daya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya gayyaci shugabannin matasan da ke shirin yin zanga-zanga a fadin kasar.

Yayin da aka ce an shirya zanga-zangar domin adawa da tsadar rayuwa, NLC ta nemi Shugaba Tinubu da ya amsa koke-koken 'yan kasar cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

"Kowa a fusace ya ke": NLC ta ba Tinubu mafita kan shirin zanga zanga

NLC ta yi magana kan masu shirin yin zanga-zanga
NLC ta ba Shugaba Tinubu shawarwari kan zanga-zangar da ake shirin yi. Hoto: @NLCHeadquarters, @officialABAT
Asali: Twitter

Shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero ne ya aika muhimmin sakon ga shugaban kasar a sanarwar da ya fitar a ranar Litinin, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zanga: NLC ta ba Tinubu shawarwari

Joe Ajaero ya ce:

“Yayin da ranar da za a gudanar da zanga-zangar ke gabatowa, NLC na kira ga Shugaba Tinubu da ya gayyaci shugabannin matasan domin tattaunawa kan korafe-korafen su.”

Shugaban na NLC ya ce hauhawar farashin kayayyaki ya karu da kashi 34.19 tare da karin kudin abinci da wutar lantarki da dai sauransu.

Joe Ajaero ya ce idan har ana neman mafita kan yunkurin matasan, to lallai akwai bukatar Shugaba Tinubu ya magance wadannan kalubale.

"Ana cikin mawuyacin hali" - NLC ga Tinubu

Jaridar The Cable ta ruwaito NLC ta ankarar da Tinubu kan cewa 'yan Najeriya na cikin mawuyacin hali inda ta ce 'yan Najeriya na da 'yancin yin zanga-zangar lumana.

Kara karanta wannan

"Akwai hannun dan Kudu:" Matasan Arewa sun janye a zanga zanga, sun yi tone tone

Ajaero ya ce yanzu gidaje da dama a Najeriya sai sun yi da kyar suke iya cin abinci ba tare da sanin idan abincin gaba zai fito ba.

Shugaban NLC ya ce zai yi matukar wahala gwamnatin tarayya ta iya danne matasan nan daga fitar da radadin da suke ji a zuciyarsu sakamakon tsare-tsaren gwamnatin.

"Babu mu a zanga-zanga" - Miyetti Allah

A wani labarin na daban, mun ruwaito cewa kungiyar Fulani makiyaya ta fadin Najeriya ta bayyana tsame kanta daga shiryayyar zanga-zangar da za a yi.

Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Abdullahi Bello-Bodejo, ya bayyana cewa babu hannunsu kuma mambobin kungiyar ba zasu fito zanga-zanga ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.