“Akwai Hannun Dan Kudu:” Matasan Arewa Sun Janye a Zanga Zanga, Sun Yi Tone Tone

“Akwai Hannun Dan Kudu:” Matasan Arewa Sun Janye a Zanga Zanga, Sun Yi Tone Tone

  • Wata kungiyar matasan Arewa ta tabbatar da janye shirinta na zanga-zanga inda ta ce akwai lauje cikin nadi daga Kudancin Najeriya
  • Shugaban kungiyar, Kwamred Murtala Garba ya ce ba su goyon bayan halin kunci da ake ciki amma sun tsame hannunsu kan haka
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani shugaban matasa kan zanga-zanga da matasa ke shirin yi a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Yayin da ake ci gaba shirye-shiryen fitowa zanga-zanga, wata kungiyar matasan Arewa ta tsame hannunta daga lamarin.

Gamayyar kungiyoyin matasan suka ce sun tsame hannunsu a zanga-zangar inda suka zargi wasu na kokarin amfani da hakan wurin kawo rigima.

Kara karanta wannan

"Ban da lalata kadarori": Tinubu ya fadi yadda ya shiga zanga zanga a lokacin soja

Matasan Arewa sun zargi neman kawo rigima a zanga-zanga
Kungiyar matasan Arewa ta tsame hannunta daga shirin zanga-zanga. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Nasiru Adamu El-hikaya.
Asali: Facebook

Zanga-zanga: Matasan Arewa sun tsame hannunsu

Shugaban kungiyar, Kwamred Murtala Garba shi ya bayyana haka ga dan jarida Nasiru Adam El-hikaya wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamred Murtala ya ce suna zargin wasu mutane sun shirya kwace ikon zanga-zangar tare da kawo tsaiko a yankin Arewa.

"Mu muka fara maganar zanga-zanga tun a watan Ramadan bayan siyan sukari da muka yi, muka ga ya yi tsada, muka ce cire tallafin nan ya jefa mutane cikin wahala."
"A haka muka fara rubuce-rubuce har muka fara samun goyon baya har daga kasashen Larabawa da China da Amurka daga 'yan Najeriya da ke can."
"Daga baya wani babban mutum daga Kudu ya kira mu Fatakwal mun je mu 53 har zuwa Asaba inda suka ce za su ba mu kudi."
"Tun farko mun so yin zanga-zanga a jihohi 36 ne amma ya ce yana so mu yi a Plateau da Kaduna da Abuja ne kawai, daga nan muka fara zargin akwai lauje cikin nadi."

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Kungiyar matasan Najeriya ta tura sako zuwa ga rassanta 104

- Kwamred Murtala Garba

Zanga-zanga: Matasa sun koka kan halin kunci

Matasan suka ce su na Allah wadai da halin da ake ciki na tsadar rayuwa amma tabbas akwai neman ta da rigima a zanga-zangar da wasu ke shirin yi.

Kwamred Garba ya ce abin da manyan mutanen daga Kudu suka fada musu abin tsoro ne wanda suke ganin akwai neman kawo rigima a Arewa.

Legit Hausa ta ji ta bakin wani shugaban matasa kan zanga-zanga da ake shirin yi a Najeriya.

Yunus Abubakar ya ce ya kamata gwamnati ta zauna ta matasa domin shawo kan lamarin madadin zanga-zanga.

Ya ce idan har za a samu maslaha shi ne abin da yafi madadin shiga zanga-zangar domin daman neman gyara ake yi.

"Ba wai nuna kin zanga-zanga ba ne amma idan za a zauna a shawo kan matsalolin shi ne yafi dacewa."

- Yunus Abubakar

Gwamna ya gargadi masu zanga-zanga

Kara karanta wannan

Hedkwatar tsaro ta jero mutanen da ake shirin kai wa hari a lokacin zanga zanga

Mun ba ku labarin cewa Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya dauki zafi kan maganar fita zanga-zanga a jihar.

Gwamna Inuwa Yahaya ya gargadi matasan ne kamar yadda Farfesa Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya yi ga matasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.