Sanusu II vs Bayero: Lauya a Kano Ya Yi Magana Bayan Kirkirar Wasu Masarautu 3 a Kano
- Fitaccen lauya mazaunin Kano, Umar Sa'ad Hassan ya bayyana matsayarsa kan kirkirar masarautu uku masu daraja ta biyu
- Lauyan ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan wannan mataki inda ya ce haan abin a yaba ne kuma zai kawo ci gaba matuka
- Hakan ya biyo bayan kirkirar masarautun Gaya da Rano da Karaye masu daraja ta biyu karkashin jagorancin Muhammadu Sanusi II
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Fitaccen lauya a Kano ya yi martani bayan kirkirar masarautu guda uku da Gwamna Abba Kabir ya yi a jihar Kano.
Lauyan mai suna Umar Sa'ad Hassan ya ce kirkirar masarautun masu daraja ta biyu abin yabawa ne kuma zai kawo ci gaba.
Kano: Lauya ya magantu kan kirkirar masarautu
Umar Sa'ad Hassan ya fadi haka ne a hirarsa da Legit inda ya ce wannan mataki na Gwamna Abba Kabir zai kara daraja da nagarta ga masarautar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II shi ne sarki mai daraja ta daya da ke sarautar masarautar jihar mai dumbin tarihi.
Lauyan ya kuma bayyana cewa rashin masarautar Bichi a cikin sababbin masarautun masu daraja ta biyu ba abin damuwa ba ne a yanzu.
"Tabbas wannan mataki na kirkirar masarautu uku a jihar Kano abin a yaba ne kuma zai kawo ci gaba a jihar."
"Dole a kare mutuncin masarautar Kano da ke dauke da sarki mai daraja ta daya da zai jagoranci sauran masarautun."
"Ba zan iya fadin tabbacin menene ya sa Bichi ba ta cikin masarautun ba amma hakan ba abin damuwa ba ne a halin yanzu."
- Umar Sa'ad Hassan
Masarautun da Gwamnan Kano, Abba ya kirkira
Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya sanya hannu a dokar kirkirar masarautu a jihar har guda uku masu daraja ta biyu.
Masarautun sun hada da Karaye da Gaya da Rano duk da haka ba a sanya masarautar Bichi a cikin wadanda aka kirkiran ba.
Aminu Ado ya ziyarci bikin saukar Alkur'ani
Kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya halarci saukar karatun Akur'ani mai girma na musamman a jihar Kano.
An gudanar da saukar Alkur'anin ne a ranar Asabar 20 ga watan Yulin 2024 a gidan marigayi Isyaka Rabiu da ke Goron Dutse.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng