Tinubu Ya Kai Aikin da Zai Taimaka Wajen Dakile Matsalar Tsaro a Mahaifar Shugaba Buhari

Tinubu Ya Kai Aikin da Zai Taimaka Wajen Dakile Matsalar Tsaro a Mahaifar Shugaba Buhari

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kai aikin babbar hanya jihar Katsina da ke Arewa maso yammacin Najeriya
  • Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya mika sakon godiya ga Bola Tinubu kan tunawa da su a wannan lokacin
  • Babban manajan kamfanin da zai yi aikin ya bayyana cewa zai yi aiki mai inganci da fadin lokaci da zai kammala

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Al'ummar jihar Katsina sun nuna farin cikinsu kan yadda shugaban kasa Bola Tinubu ya tuna da su.

Bola Tinubu zai gabatar da aikin hanya ne a jihar Katsina da ta kutsa cikin ƙananan hukumomi daban-daban.

Kara karanta wannan

Matasa na shirye shiryen zanga zanga, Tinubu zai taho Arewa domin raba tallafi

Tinubu Bola
Sarkin Katsina ya mika godiya ga Tinubu bisa aikin titi. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya mika godiya ga shugaba Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda hanyar za ta kasance a Katsina

Rahoton Arise News ya nuna cewa hanyar za ta kasance mai nisan kilomita 147 kuma za ta ratsa ta Mararabar Kankara, ta shiga Katsina sannan ta shiga Dutsim-ma.

Ana san ran cewa hanyar za ta bunkasa tattalin yankin tare da taimakawa wajen yaki da yan bindiga masu tare mutane idan hanya ba ta da kyau.

Al'ummar Katsina sun yabi Bola Tinubu

A madadin al'ummar jihar Katsina, mai martaba Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya mika godiya ga shugaba Bola Tinubu kan aikin.

Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya ya bukaci ma su aikin da su yi aiki mai inganci da al'ummar jihar za su mora.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: An fadawa Tinubu sirri 3 domin shawo kan talakan Najeriya cikin sauki

Yaushe za a kammala titin a Katsina?

Babban manajan kamfanin titin da zai yi aikin, Injiniya Doumit Ters ya bayyana cewa za su yi aiki yadda ya kamata.

Doumit Ters ya tabbatar da cewa za su kammala aikin hanyar ne cikin watanni 12 kuma al'umma za su fara morar aikin nan take.

Zanga zanga: Matasa sun goyi bayan Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa wasu matasan yankin Arewa ta Tsakiya sun nesanta kansu daga zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar nan.

Matasan sun bayyana cewa a cikin shekara ɗaya, Shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya samu nasarori masu yawa da bai kamata a yi zanga zanga ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng