Sanata Ya Ce Albashin 'Yan Majalisa Ya Yi Kadan Bayan Jin Za a Fara Biyan Ma’aikata N70,000

Sanata Ya Ce Albashin 'Yan Majalisa Ya Yi Kadan Bayan Jin Za a Fara Biyan Ma’aikata N70,000

  • Sanata wai wakiltar jihar Anambara, Orji Uzo Kalu ya koka kan yadda ake biyan Sanatoci kudin kadan a matsayin albashi
  • Bayan haka, Sanata Orji ya bukaci a canza tsarin zaman majalisa yadda zai dace da kudin da ake biyansu a matsayin albashi
  • Senator Kalu ya yi kira na musamman ga shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kan amincewa da canza tsarin majalisar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sanata Orji Uzo Kalu ya nuna damuwa kan yadda ake biyan Sanatocin Najeriya albashi kaɗan.

A karkashin haka, Orji Kalu ya bukaci shugaban kasa da shugabannin majalisa su canza tsarin zaman majalisar.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Bayan Ali Ndume, Sanata ya kara cire tsoro ya fadawa Tinubu gaskiya

Sanata Kalu
Sanata ya koka kan karancin albashi. Hoto: Senator Orji Uzo Kalu
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan da Sanata Orji Uzo Kalu ya yi ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Albashinmu ya yi ƙadan' - Sanata Orji Kalu

Sanata Orji Uzo Kalu ya bayyana cewa a mutane suna dauka ana biyansu kudi sosai amma a zahiri kudin ya musu kadan sosai.

Amma rahoton Premium Times ya nuna cewa ana biyan kowane Sanata kusan N1m a wata da kuma kudin gudanar da ayyukan ofis kimanin N13.5 duk wata.

Tsarin da Sanata Kalu yake so a dawo

Kasancewar ya ce ba a ba su kuɗi sosai, Orji Kalu ya bukaci a rage musu yawan zaman da suke yi zuwa watanni uku.

Sanatan ya ce idan aka dawo da su zaman watanni uku bai wuce su rika zama sau hudu a shekara ba sai dai idan akwai buƙata ta musamman.

Kara karanta wannan

N70,000: Kalubale 5 da ke gaban 'yan kwadago da ma'aikata bayan karin albashi

Sanata Kalu ya yi kira ga Tinubu

Sanata Orji Uzo Kalu ya yi kira shugaban kasa Bola Tinubu kan amincewa da shawarin da ya kawo.

Ya bayyana cewa rage kwanakin zai kawo amfani ga ƙasa sosai ta yadda za a rage kudin da ake kashewa wajen gudanar da gwamnati.

Gwamnan Osun zai biya ma'aikata N70,000

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Osun ya yi alkawarin biyan ma'aikatan jihar sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 da gwamnatin tarayya da ƴan ƙwadago suka amince da shi

Gwamna Ademola Adeleke ta hannun kwamishinan yaɗa labaransa ya bayyana cewa walwalar ma'aikata na daga cikin abin da yake ba da fifiko a kai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng