Ana Kukan Babu, Dan Majalisar Katsina ya Gwangwaje Yan Mazabarsa da Miliyoyi
- Dan majalisa mai wakiltar Musawa/Matazu a jihar Katsina Abdullahi Aliyu ya gwangwaje masu sana'o'i a mazabarsa da kudi da kayan noma
- Mutane 70 ne su ka samu tallafin N500,000 a wani yunkuri na bunkasa sana'arsu da rage radadin rayuwa yayin da ya raba takin zamani
- Dan majalisa Abdullahi Aliyu Ahmed ya ce ya na kyautata zaton rabon tallafin zai kawo sauki tare da dadaɗawa jama'arsa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina - Masu sana'o'i a mazabar Musawa/Matazu da ke jihar Katsina sun samu tagomashin tallafi daga dan majalisarsu, Abdullahi Ahmed Aliyu da zummar bunkasa sana'arsu.
Mutanen mazabar guda 70 ne su ka samu tallafin bunkasa sana'o'i na N500,000 a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke kukan rashin abin hannu.
Jaridar The Guardian ta tattaro cewa masu cikakken bayanin kasuwancin da su ke yi ne kadai su ka samu tallafin a wani yunkuri na bunkasa harkokin sana'arsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan majalisa ya bayar da tallafin N35m
Dan majalisar tarayya mai wakiltar Musawa/Matazu a jihar Katsina, Abdullahi Aliyu Ahmed ya ba wa masu kasuwanci a yankinsa kyautar Naira Miliyan 35 domin habaka ayyukansu. Jaridar Independent ta wallafa cewa dan majalisar ya ce ya bayar da tallafin ne domin saukaka wa mutane halin da su ke ciki.
Dan majalisa ya raba karin tallafi
Haka kuma dan majalisar ya raba kayan noma ga manoma da ke zaune a mazabar Musawa/Matazu ciki har da taki buhu 2, 500 yayin da noma ya kankama. Hon. Abdullahi Aliyu Ahmed ya kuma raba keken guragu ga masu bukata ta musamman da ke mazabarsa, inda ya bayyana kyakkyawan zaton abubuwan da aka raba za su taimaki jama'a.
Gwamna ya raba tallafin abinci
A wani labarin kuma gwamnatin Borno ta raba tallafin kayan abinci ga iyalai N70,000 da ke zaune a yankin Bama na jihar domin rage yunwa. Gwamna Babagana Umara Zulum ne ya yi rabon kayan abincin ga iyalan marasa gata, masu karamin karfi da gajiyayyu, sannan an raba kudade da zannuwa ga mata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng