Sarautar Kano: Rikici Ya Ɓarke a Taron da Aminu Ado Ya Halarta, An Farmaki Ɗan Majalisar NNPP
- Ƴan daba sun farmaki ɗan majalisar dokokin Kano a wurin taron saukar Alkur'ani wanda Aminu Ado Bayero ya halarta ranar Asabar
- Hon Abdul-Majid Umar ya yi zargin cewa ƴan daban suna cikin tawagar sarki na 15 da aka tuɓe, zargin da hadimin basaraken ya musanta
- Ɗan majalisar ya ce ƴan daban sun farmake shi ne yayin da ya fito daga Masallacin kuma sun jikkata mutanensa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Ƴan daba sun yi yunƙurin lakaɗawa ɗan majalisar dokokin jihar Kano dukan tsiya a wurin taron saukar Alkur'ani wanda sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya halarta.
Ɗan majalisar mai wakiltar Gwale a inuwar NNPP, Abdul-Majid Umar, ya sha da ƙyar a wurin taron na ranar Asabar a Masallacin Khalifa Isiyaka Rabiu.
Da yake hira da BBC Hausa ranar Litinin, ɗan majalisar ya bayyana cewa Aminu Ado da ƴan sanda ne suka kuɓutar da shi daga ƴunkurin fadawa da wasu mutane.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aminu Ado ya halarci taro a Kano
Aminu Ado Bayero ya halarci rufe taron addu'o'in neman zaman lafiya wanda Malaman Tijjaniyya suka saba shiryawa a gidan Isiyaka Rabi'u da ke yankin Gwale.
Abdul-Majid Umar ya zauna a gefen Sarki na 15 Aminu Ado Bayero kuma yana fita daga ɗakin taron ƴan daban suka yo kansa, Premium Times ta ruwaito.
Ɗan majalisar ya zargi tawagar Aminu
Ɗan majalisar ya yi zargin cewa dubban magoya bayan sarkin wanda aka tsige ne suka farmake shi, wanda ya tilasta masa barin wurin babu shiri.
A kalamansa, Abdul-Majid Umar wanda aka fi sani da Mai rigar fata ya ce:
"Tun daga shigowa aka sami wasu daga cikin fadawa suka fara zagi da maganganu marasa daɗi cewa mu ƴan majalisa musammanin ni da muka yi doka aka rusa masarautu sai sun yi kaza da kaza."
"Shi kansa (Aminu Ado Bayero) sai da ya tunkuɗe wani bafade da ya kai hannu zai kama ni a taron."
Yadda ƴan daba suka farmaki ɗan majalisa
Abdul-Majid ya ƙara da cewa ya nemi uzurin barin wurin taron bayan ya fahimci shi kaɗai ne jami'in gwamnatin Kano a wurin amma yana fitowa lamarin ya ƙara rincaɓewa.
A cewarsa, yana fitowa harabar masallacin ya ci karo da dubban ƴan daba ɗauke da mugayen makamai sun yo ƙansa, hakan ya sa ya yi gaggawar faɗawa motar ƴan sanda.
"Sun jefi biyu daga cikin mutanen da nake tare da su, ɗaya kuma an sare shi a ƙafa," in ji shi.
Sai dai daya daga cikin hadiman sarkin da aka tube, Khalid Adamu, ya musanta cewa ƴan daban suna cikin tawagar Aminu Ado Bayero.
Gwamnatin Kano za ta shiya zaɓen ciyamomi
A wani rahoton Gwamnatin Kano ta bayyana cewa za ta mutunta hukuncin kotun koli kan tabbatar wa kananan hukumomi 'yancin gashin kansu.
Darakta Janar kan yada labaran gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya kara da cewa gwamnati ta shirya gudanar da zaben kananan hukumomi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng