Matatar Dangote: Majalisa Ta Dauki Mataki Ganin An Samu Sabani da Gwamnatin Tarayya

Matatar Dangote: Majalisa Ta Dauki Mataki Ganin An Samu Sabani da Gwamnatin Tarayya

  • Majalisar wakilai ta yanke hukuncin gayyatar Alhaji Aliko Dangote da hukumar NMDPRA a gabanta domin gano kan sabaninsu
  • A yau Litinin ne majalisar wakilai ta bayyana haka yayin da take tattaunawa a kan takaddamar da ta barke a tsakaninsu kan matatar man Dangote
  • Haka zalika majalisar ta yi bayani kan yadda ya kamata su cigaba da mu'amala da juna har zuwa lokacin da za su gurfana a majalisar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Majalisar wakilan Najeriya ta yi shiga tsakani bayan rikicin da ya barke tsakanin gwamnatin tarayya da Dangote.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta zargi Dangote da rashin samar da ingantaccen mai a matarsa da ke Legas.

Kara karanta wannan

"Ba domin cin mutunci ba ne": Gwamna ya fadi dalilin gyara a dokar masarautu

Majalisa
Majalisa ta dauki mataki kan rikicin matatar man Dangote. Hoto: Abbas Tajudden|Dangote Industries
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa majalisar za ta gayyaci dukkan masu ruwa da tsaki domin tantance gaskiyar lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa za ta gayyaci Dangote da NMDPRA

Majalisar wakilai ta ce a yau za ta tura takardun gayyata ga dukkan masu ruwa da tsaki a kan harkar man fetur domin gano gaskiya kan rikicin matatar man Dangote.

Cikin waɗanda za a gayyata akwai kamfanonin samar da man fetur, kungiyar IPMAN, masu saye da sayar da man fetur da dai sauransu.

Me za a bincika wajen zama da Dangote?

Bayan rikici tsakanin Dangote da hukumar NMDPRA, zaman zai hada da bincike kan tsadar man fetur a Najeriya da masu shiga tsakiya su lalata lamura.

Haka zalika za a binciki dalilin shigo da danyen mai daga waje da Dangote yake duk da cewa akwai shi a Najeriya da yadda ake ba kamfanonin mai lasisi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa ta yi babbar barna a jihar Arewa, mutum 1,664 sun rasa matsugunni

Kiran majalisa ga Dangote da NMDPRA

Biyo bayan matakin da majalisar ta dauka ta yi kira ga Dangote da hukumar NMDPRA kan cewa su mayar da wuƙaƙensu.

Rahoton the Cable ya nuna cewa majalisar ta ce dukkan waɗanda suke rikici kan man fetur su dakata har sai majalisa ta kammala bincike.

Yan majalisa sun ziyarci matatar Dangote

A wani rahoton, kun ji cewa, jagororin majalisar wakilai karkashin Rt. Hon Tajudeen Abbas sun kai ziyara matatar Ɗangote da ke yankin Lekki a jihar Legas.

Ƴan majalisar sun kai wannan ziyara ne domin duba yadda aikin matatar ke tafiya yayin da take shirin fara sayar da man fetur a watan Agusta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng