Daga Zuwa a Tura Masa N2, 500, Mutumi Ya Wawushewa Mai POS N360, 000 a Akawun
- Wani matashi mai sana'ar sayar da babura da POS a jihar Sokoto ya gamu da sharrin barawo har wajen sana'arsa
- Matashin mai suna Buhari Haruna ya shaida wa Legit cewa sau biyu matashin da ya zarga da sace masa POS na ziyartar shagonsa
- Ya ce matashin da ya ke kyautata zaton sunansa Gaddafi ya yi zuwan farko ne a ranar Asabar, sannan ya dawo ranar Lahadi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto - Wani matashi mazaunin Sokoto, Buhari Haruna ya nemi daukin jama'a kan gano wanda ya sace masa na'urar kudi ta POS har wurin sana'arsa.
Buhari Haruna, wanda ke sayar da babura a karamar hukumar Illela ya ce matashin mai suna Gaddafi Zakaria ya shammace shi kafin ya dauke POS din.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Buhari Haruna ya ce sau biyu Gaddafi ya na zuwa shagonsa a cikin kwanaki biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda matashin ya sace POS a Sokoto
Buhari Haruna a zantawarsa da Legit ya ce a ranar Asabar wani matashi ya zo neman a tura masa kudi N2,500, inda aka kammala hada-hada ba tare da cikas ba.
Amma matashin ya sake dawo wa ranar Lahadi - ranar kasuwa domin zai tura kudi, kuma shi Haruna ya rubuta masa lambar akawun.
"Da na rubuta masa lambar akawun, dama aiki ya yi mani yawa sai na shiga daga cikin shago na bar POS din a waje a kan tebur."
"Sai wani ya turo min kudi 361, 500 dama ina da mahajar asusun a waya ta, kawai da na duba sai na ga ya riga ya cire kudin ya tura a lambar shi palmpay Gaddafi Zakaria."
-Buhari Haruna
Matashi ya dauki mataki bayan sace POS
Buhari Haruna ya ce yanzu haka ya dauki matakin toshe daukar kudi ta na'urar POS dinsa da aka sace, amma ya na bukatar taimako.
Ya shawarci duk wadanda su ka yi ido hudu da Gaddafi ko su ka san shi su gaggauta tuntubarsa domin daukar mataki na gaba.
Likitan Bogi ya damfari matashiya mai POS
A baya kun ji labarin yadda wani likitan bogi, Igwe Gift Okechukwu ya shiga hannun yan sanda bayan tafka gagarumar damfara da ya yiwa mai sana'ar POS a Owerri.
Rundunar yan sandan Owerri ta damke Igwe Gift Okechukwu da ake zargi da damfarar Anita Chinwe Mathias makudan kudi har N21m, gami da wasu laifukan da su ka hada da zamba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng