"Ku Shirya," Kungiyar Amnesty Int'l ta Tura Sako ga Gwamnati kan Zanga Zanga
- Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta shawarci gwamnatin Najeriya kan yadda za ta bullo wa batun zanga-zanga
- Shugaban kungiyar na Najeriya, Mista Isa Sanusi ya shaida wa Legit cewa ba a hana zanga-zanga idan jama'a sun ce za su yi ba
- Amma ya bayyana cewa akwai matakai da gwamnatin tarayya ya kamata ta dauka domin dakile rikidersa wa zuwa tashin hankali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International (AI) ta shawarci gwamnatin tarayya kan yadda za ta bullowa lamarin zanga-zanga da wasu ke shirin yi a kasar nan.
A tattaunawar shugaban kungiyar na Najeriya, Isa Sanusi da Legit, ya ce gudanar da zanga-zanga ba haramun ba ce, kuma akwai nauyi da ya rataya a wuyan gwamnati a irin lokutan.
Shugaban Amnesty Int'l ya ce dole ne gwamnatin tarayya da jami'an tsaro su tabbatar an kare rayuka da duniyoyin masu gudanar da zanga-zanga, idan har hakan ta kasance.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Zanga zanga ba haramun ba ce," Amnesty Int'l
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce ba ta dauki zanga-zanga a matsayin abu mai illa ba.
Shugaban kungiyar na kasar nan, Isa Sanusi ya ce tsarin mulkin Najeriya bai haramta a gudanar da zanga-zanga ba, amma dai akwai sharuda.
Ya ce sharadin shi ne ya zama zama zanga-zanga ce ta lumana wacce ba sace-sace, babu kona dukiya, babu zage-zage, babu hauragiya.
"Sannan ita ma gwamnati ta na da hakki. Domin idan mutum ya ce zai yi zanga-zanga, hakkin gwamnati ne ta ba shi kariya, sannan ta tabbatar da cewar ya yi ta a cikin lumana ba tare da wani ya zo ya shiga ciki ya bata masa zanga-zangar ba kuma ta zo ta rikide ta zama tashin hankali."
-Isa Sanusi, Shugaban AI na Najeriya.
"Ba a hana zanga-zanga," Amnesty Int'l
Kungiyar AI ta shawarci gwamnatin Najeriya kan cewa ba hana zanga-zanga ake yi ba idan jama'a sun kuduri aniyar gudanar da ita.
Shugaban kungiyar na kasa ya ce kokari ake yi a nusar da jama'a yadda za su gudanar da ita cikin lumana da kwanciyar hankali tare da kare lafiyarsu.
Katsina: An yi zanga-zanga kan rashin tsaro
A wani rahoton kun ji cewa wasu mazauna karamar hukumar Kankara a jihar Katsina sun gudanar da zanga-zanga kan rashin tsaro da ya hana su sakat.
Mazauna yankin sun rufe manyan hanyoyin da ake bi a bangarensu ciki har da mararrabar Katsina zuwa Kano, tare da bukatar mahukunta su gaggauta kawo masu agaji kan yan ta'adda.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng