“A Daina Alakanta Ni Da ’Yan Bindiga”: Matawalle Ya Yi Magana Kan Bidiyon Bello Turji
- Tsohon gwamnan Zamfara kuma ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya zargi makiya da haɗa wani bidiyo dake yawo na Bello Turji
- Yace gwamnatin PDP a jihar ke son ɓata masa suna kuma wannan bidiyon cike da rashin ƙwarewa aka shirya shi
- Bello Matawalle ya ce bashi da hannu a ta'addanci don haka ne ma yasa hukumomin tsaro suka bincikesa kafin a naɗa shi ministan Tinubu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara - Karamin ministan tsaro, Muhammad Bello Matawalle, ya ja kunnen abokan adawarsa a siyasa da su guji alaƙanta shi da lamurran Bello Turji.
A wata takardar da ofishin ministan ya fitar ranar Lahadi, Matawalle ya zargi wasu a cikin gwamnatin Zamfara da shirya labarai kan matsalar tsaron jihar tare da danganta masa.
Matawalle yayi martani ne kan wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya inda ake bayyana alaƙarsa da lamurran 'yan bindiga a jiharsa ta Zamfara, jaridar Leadership ta bayyana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Gwamnati PDP ke son ganin bayana" - Matawalle
Takamaimai, tsohon gwamnan na Zamfara ya zargi gwamnatin PDP mai ci yanzu a jihar da shirya bata masa suna alhalin bashi da wani laifi.
"Muryar Bello Turjin dake yawo bata fita sosai ba kuma an gyara ta ne da wani bidiyo wanda ake zargin tsohon gwamnan da rashin adalci a sasancin da gwamnatinsa ta yi da 'yan bindiga.
"Rashin kwarewar editan bidiyo/murya ya fito fili ta yadda mutum zai iya lura da rashin daidaituwar murya da kuma hoton bidiyon a lokacin da Bello Turji ke magana.
- A cewar sanarwar.
"Bani da hannu a ta'addanci" - Matawalle
Mawatalle ya ce wannan duk aikin wadanda ya kira da makiyan jihar Zamfara da makiyan cigaban Najeriya wadanda ke sukar nadin da shugaba Bola Tinubu yayi masa ne.
Tsohon gwamnan na Zamfara ya ƙara da cewa an tantanceshi a fannin tsaro kafin tabbatar masa da nadin ministan.
Ya jadda cewa wannan bidiyon da ake yadawa an shirya shi ne ba tare da ƙwarewa ba domin bata sunansa, don haka jama'a su yi watsi da shi.
Bello Turji ya zargi Matawalle da ta'addanci
A wani labari na daban, mun bayyana muku cewa shahararren ɗan bindiga, Bello Turji, ya zargi tsohon gwamnan Zamfara kuma ƙaramin ministan tsaro da hannu a ta'addanci.
A wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an ga gagararren ɗan bindigan na alaƙanta ta'addanci dake faruwa a jihar da Bello Muhammad Matawalle.
Asali: Legit.ng