Abin da Aminu Ado Ya Fadawa Dan Agundi a Waya Bayan Tinubu Ya Ba Shi Mukami
- Kwanaki kadan bayan Bola Tinubu ya nada Baffa Dan Agundi mukami, Aminu Ado Bayero ya yi martani kan nadin
- Sarkin Kano na 15 ya taya Dan Agundi murnar samun mukamin inda ya ce tabbas an yi nadin a inda ya fi dacewa
- Aminu Ado ya shawarci Dan Agundi ya yi amfani da kwarewarsa wurin gudanar da shugabancin hukumar da tsoron Allah
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi martani bayan nada Baffa Dan Agundi mukami a Najeriya.
Aminu Ado ya taya Dan Agundi murnar samun mukamin shugaban hukumar inganci da nagartar ayyuka ta NPC.
Aminu Ado ya kira Dan Agundi a waya
Tsohon sarkin ya taya Dan Agundi murnar bayan ya kiransa wayar salula inda ya yi masa fatan alheri, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aminu Ado ya ce tabbas an yi nadin ga wanda ya dace duba da tarun kwarewa da Dan Agundi ya ke da shi a mukaman da ya rike.
"Tabbas an nada Dan Agundi a inda ya dace, mun ga irin kokarinka a lokacin da ka rike mukadashin daraktan hukumar CPC a Kano."
"Ka yi matukar kokari cikin kwarewa wurin tabbatar da yaki da miyagun kwayoyi da magunguna marasa inganci da wadanda suka lalace."
"Ka tabbatar da kwarewarka lokacin da ka ke hukumar kula da hanyoyi a Kano yayin da ka samar da kudaden shiga ga jihar."
- Aminu Ado Bayero
Aminu Ado ya shawari Dan Agundi
Aminu Ado ya yi godiya ta musamman ga Shugaba Bola Tinubu kan wannan nadin inda ya ce Dan Agundi zai yi nasara.
Ya ba Dan Agundi shawara da ya kasance mai hakuri tare da gudanar da shugabancin hukumar cikin tsoron Allah da gaskiya.
Tinubu ya nada Dan Agundi mukami
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Baffa Babba Dan Agundi a matsayin shugaban hukumar NPC.
Dan Agundi zai jagoranci hukumar kula da nagarta da ingancin ayyuka domin kawo sauyi da kuma sabbin tsare-tsare.
Asali: Legit.ng