“Na Yi Mamakin Ganin Abin da Ban Yi Tsammani Ba”: Rarara Kan Sace Mahaifiyarsa
- Mawakin siyasa a Arewacin Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya fitar da wani faifan bidiyo domin godiya ga al'umma
- Rarara ya ce ya sha mamaki ganin yadda jami'an tsaro suke kokari musamman a bangaren tsaro da ceto al'ummar kasar
- Mawakin ya godewa shugaban kasa, Bola Tinubu da matarsa da kuma Nuhu Ribadu da jama'a da suka taimaka da addu'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Fitaccen mawakin siyasa a Arewacin Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana yadda ya sha mamaki kan ta'addanci a kasar.
Mawakin ya ce akwai abubuwan da suka faru wanda bai taba sani ba har sai da aka sace mahaifiyarsa ya san da su.
Rarara ya tura sakon godiya ga al'umma
Rarara ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo na godiya a shafinsa na Facebook bayan sako mahafiyarsa, Hauwa Adamu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin faifan bidiyon, ya yi godiya ga al'umma musamman wadanda suka taya su da addu'o'i domin ganin an ceto mahaifiyarsa.
"Ina mika godiya ga jami'an tsaron Najeriya saboda wallahi ni naga abubuwan da a da ban ma san da su ba sai yanzu."
"Daman an ce sai wani abu ya same ka za ka ga wani abin, daga kama mama zuwa fitowarta da idona naga an fitar da mutane sun kai 800."
- Dauda Kahutu Rarara
Abin da Rarara ya gani da idonsa
"Ni na gani da idona saboda na shiga harkar ko kuma ana nunamin irin kokarin da ake yi a bangaren tsaro."
"Da ban shiga ba, ba zan san ana yi ba, amma yanzu Alhamdulillahi yanzu na sani ina kara godiya ga shi shugaban kasa."
- Dauda Kahutu Rarara
Yadda Kirista ya taimaki mahaifiyar Rarara
Kun ji cewa mawakin siyasa a Arewacin Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya yi godiya ga wadanda suka taya su da addu'o'i bayan sace mahaifiyarsa.
Rarara ya ce ya sha mamaki bayan wani Kirista ya sadaukar da rayuwarsa a hannun 'yan bindiga domin kawai ya taimaki mahaifiyarsa, Hauwa Adamu.
Asali: Legit.ng