Gwamna Ya Yi Gargadi, Zai Kakaba Harajin Ajiye Ababen Hawa a Masallatai da Coci

Gwamna Ya Yi Gargadi, Zai Kakaba Harajin Ajiye Ababen Hawa a Masallatai da Coci

  • Gwamnatin jihar Lagos ta shirya kakaba karbar haraji kan masu ajiye ababan hawa a wuraren ibada da sauran hanyoyi
  • Gwamnatin ta tabbatar da cewa za ta fara karbar harajin nan da watan Oktobar wannan shekara ta 2024 da muke ciki
  • Hukumar kula da ajiye ababan hawa a jihar ta LASPA ita ta tabbatar da haka ta bakin daraktan ayyuka, Ayokunle Akinrimisi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Gwamnatin jihar Lagos za ta kaddamar da karbar haraji yayin ajiye ababan hawa a wuraren ibada.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa dokar za ta fara aiki ne a watan Oktoban wannan shekara ta 2024 da muke ciki.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun soki Ministan Buhari kan goyon bayan zanga zanga

Gwamnatin Lagos za ta fara karbar haraji a masallatai da coci
Gwamnatin Lagos za ta kakaba karbar haraji kan masu ajiye ababan hawa a masallaci da coci. Hoto: Babajide Sanwo-Olu.
Asali: Twitter

Lagos za ta kakaba haraji a masallaci

Shugaban sashen ayyuka na hukumar adana ababan hawa (LASPA), Ayokunle Akinrimisi shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da Vanguard ta samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akinrimisi ya ce za a fara karbar harajin ne kowace awa da aka ajiye abun hawan a kan tituna da kuma wuraren ibada.

Har ila yau, ya ce za a dauki tsauraran matakai kan wadanda ke ajiye ababawan hawa ba bisa ka'ida ba a kan hanyoyi.

"Ina mai sanar da ku cewa hukumarmu za ta fara kawo sauyi game da ajiye ababan hawa a kan hanyoyin birnin Lagos."
"Ababan hawa da aka ajiye a coci-coci za su fara biyan kudi kowane awa kuma duk wadanda ke saba ka'aida za su fuskanci hukunci."

- Ayokunle Akinrimisi

Gwamnatin Lagos ta gargadi masu saba doka

Kara karanta wannan

Fusataccen malamin addini ya zane mabiyansa kan saba doka, sun sha mamaki

Hukumar ta kuma gargadi jama'a da su tabbatar sun bi dokar da aka gindaya wurin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Sai dai kuma hukumar ba ta bayyana yawan kudin da za a rika biya ba bayan ajiye ababan hawan a cikin birnin.

Sanwo-Olu ya ba matasan NYSC kyautar N100,000

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos ya gwangwaje matasa masu bautar kasa da kyautar kudi.

Sanwo-Olu ya ba kowane matashi da ya kammla karbar horaswa a sansanin NYSC kyautar N100,000 domin tallafawa kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.