Mafi Karancin Albashi: Jerin Gwamnonin da Suka Amince Za Su Biya N70,000
- Biyo bayan sanarwar Shugaba Bola Tinubu na ayyana N70,000 matsayin sabon albashi, wasu gwamnoni sun amince da hakan
- Wadannan gwamnonin sun yi alkawarin fifita jin dadin ma’aikatansu tare da aiwatar da biyan sabon mafi karancin albashin
- Yayin da irinsu gwamnan Osun suka amince, har yanzu wasu gwamnonin ba su yanke shawara kan sabon mafi karancin albashi ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja, FCT – Bayan yarjejeniyar Shugaba Bola Tinubu da 'yan kwadago na biyan N70,000 matsayin sabon mafi karancin albashi, yanzu hankali ya koma kan gwamnonin jihohi.
Ya zuwa yanzu dai gwamnoni da dama ba su yanke shawara kan sabon mafi karancin albashin da gwamnatin tarayya ta yanke ba.
Sai dai akwai wasu gwamnonin da suka amince da biyan N70,000 matsayin sabon mafi karancin albashin. Ga jerin su a nan kasa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Gwamnan Osun zai biya ma'aikata N70,000
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya ce gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000 ga ma’aikatan jihar.
Mun ruwaito cewa Adeleke ya yi alkawarin ba da fifiko ga jin dadin ma’aikata a jihar ta Kudu maso Yamma.
Kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a na jihar, Kolapo Alimi ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 19 ga watan Yuli.
2. Sabon albashi: Gwamna Alia ya yanke shawara
Hakazalika, Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue ya ce gwamnatinsa a shirye take ta biya ma’aikatan jihar sabon mafi karancin albashi na N70,000.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne muka ruwaito cewa gwamnan ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Makurdi, babban birnin jihar.
Ya lura cewa gwamnatinsa ta toshe duk wata kafar matsaloli kuma ta aiwatar da matakan da suka dace don ganin abubuwa su yi kyau.
3. Gwamna Uno na Akwa Ibom zai biya N70,000
Ita ma gwamnatin jihar Akwa Ibom ta ce ta amince kuma a shirye take ta biya sabon mafi karancin albashi na N70,000.
Gwamna Umo Eno ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta bi yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kungiyoyin kwadago da gwamnatin tarayya.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa shugaban ma’aikatan jihar, Effiong Essien, ya tabbatar da matsayin gwamnan a Uyo.
4. Makinde: "Biyan N70,00 ba zai yi wahala ba"
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana kwarin gwiwar cewa aiwatar da mafi karancin albashi na N70,000 da gwamnatin tarayya ta amince da shi ba zai yi wahala ba.
A ranar Juma’a, Sulaimon Olanrewaju, babban sakataren yada labaran gwamnan, ya bayyana hakan ga manema labarai, inji wani rahoton jaridar The Nation.
Olanrewaju ya tuna cewa yayin bikin ranar ma’aikata ta 2024, gwamnan ya yi alkawarin biyan duk wani mafi karancin albashi da gwamnatin tarayyar ta amince da shi.
Yadda ake bin diddigin kudin FAAC
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan Najeriya yanzu na iya bibiyar kudin da asusun rabon kudi na tarayya (FAAC) ke turawa kananan hukumomin kasar nan.
Hakan zai ba 'yan Najeriya damar sanin kudin da suka samu da kuma bibiyar ayyukan da kowanne shugaban karamar hukuma ya yi domin su yi alkalanci.
Asali: Legit.ng