“Ba Mu Bukatar Shikafarka”: Malamin Musulunci Ya Nemi Bukata 1 Wurin Tinubu

“Ba Mu Bukatar Shikafarka”: Malamin Musulunci Ya Nemi Bukata 1 Wurin Tinubu

  • Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Muhamamd Adam Albaniy ya yi tsokaci kan shirin raba tirelolin shinkaka a Najeriya
  • Sheikh Albaniy ya ce kwata-kwata raba shinkafa ba shi ne mafita ba abin da ya kamata a yi shi ne kawai dawo da tallafin mai
  • Wannan na zuwa ne yayin da 'yan kasar ke cikin mawuyacin hali wanda ya tilasta matasa shirin fara zanga-zanga a fadin kasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Adam Muhammad Albaniy ya magantu kan halin kunci da ake ciki.

Malamin ya ce hanya daya ce ta dakile halin kunci da ake ciki shi ne dawo da tallafin mai ba wai raba shinkafa ba.

Kara karanta wannan

Shin da gaske an aikawa malamai N16m domin hana matasa zanga-zanga a Arewa?

Malamin addini ya ba Tinubu shawara kan halin kunci
Sheikh Muhammad Adam Albani ya bukaci dawo da tallafi madadin raba shinakafa. Hoto: Sheikh Adam Muhammad Albaniy Gombe.
Asali: Facebook

Albaniy ya fadi babbar matsalar 'yan Najeriya

Albanin Gombe ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya Asabar 20 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce babban matsalar 'yan Najeriya yanzu shi ne dawo da tallafi saboda shi ne ya jefa al'umma cikin mummnan yanayi.

Har ila yau, malamin ya ja kunnen Shugaba Bola Tinubu kada ya amince da masu ce masa abubuwa suna daidaita.

Albaniy ya ba Tinubu shawara kan tallafi

"Daga cikin manyan abubuwa da ya damu 'yan Najeriya abu biyu ne, na farko a dawo da tallafin da aka janye."
"Duk wani tsari da aka kawo a kasar ana yi ne domin samar da sauki, saboda haka duk tsarin da ya zama sharri babu dalilin manne masa cewa sai an ci gaba da tafiya kansa ba."

Kara karanta wannan

Jawabin da ya ceci Sarkin Gaya, Gwamnan Kano ya dawo da shi da aka kirkiro masarautu

"Idan har sun yi haka ne domin samar da sauki, to abin ya juya, manufarku ba ta tabbata ba, to ya kamata ku dawo da shi tun da ba ayar Al'kur'ani ba ce bare a ce ba za a goge ta ba."

- Sheikh Albani

Sheikh Albani ya ce raba shinaka tirela 20 ba mafita ba ce inda ya ce duk wanda ke fadawa Bola Tinubu abubuwa sun daidaita karya ne.

Albaniy zai tunkari matasa a mimbari

Kun ji cewa Sheikh Adam Albaniy ya yi martani a kan maganganun da ake yaɗawa kan fada da limaman Jumu'a idan suka yi hani da zanga zanga.

Albanin Gombe ya ce yana daidai da duk wani maras kunya da zai tunkare shi domin ya yi magana a kan hana wani abu yayin huɗubar Jumu'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.