Zanga Zanga: Halin da Matashin da Ya Yi Hudubar Jefo Malamai Daga Mimbari Yake Ciki
- Matashin da ya yi hudubar jefo malamai masu hana zanga-zanga daga minbari ya gamu da matsala bayan jefa shi gidan yari
- An cafke Junaidu Abdullahi tun a ranar Laraba inda aka wuce da shi Abuja kafin daga bisani aka gano shi a gidan yarin Kurmawa a Kano
- An tsare matashin da aka fi sani da Abusalma a gidan kason Kurmawa zuwa lokacin shari'a nan da makwanni uku masu zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - An tasa keyar dan TikTok, Junaidu Abdullahi a gidan kaso kan hudubar zanga-zanga ga matasa a Najeriya.
Matashin da aka fi sani da Abusalma shi ne ya ce duk malamin da ya hana zanga-zanga a jefo shi daga mimbarin wa'azi.
Zanga-zanga: An tsare Abusalma a gidan kaso
Daily Nigerian ta ruwaito cewa an an kama Abusalma tun ranar Laraba 17 ga watan Yulin 2024 inda aka wuce da shi Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani dan uwan Abusalma mai suna Mustapha Hamza ya tabbatar da haka inda ya yanzu haka yana tsare a gidan yarin Kurmawa da ke Kano.
Hakan ya biyo bayan hudubar Abusalma cewa a rikito da malaman da ke hana zanga-zanga daga mimbari wanda ya jawo zazzafan martani daga malaman.
Halin da Abusalma ke ciki a yanzu
"Ya bar gida a ranar Laraba da safe bayan samun kiran gagawa da misalin karfe 8:00 inda ko karyawa bai yi ba, wannan shi ne karshen gani na da shi."
"Mun kai rahoto ofishin 'yan sanda inda suka kira sauran ofisoshinsu da tabbatar da cewa ya bata."
"Yayin da muke ci gaba da nemansa, na samu kira cewa Junaidu yana gidan yarin Kurmawa inda ake jiran shari'ar sai nan da makwanni uku."
- Mustapha Hamza
Malamin Musulunci ya yi fariya kan zanga-zanga
Kun ji cewa Malamin Musulunci, Sheikh Muhammad Auwal Albaniy ya yi gargadi ga masu cewa za su jefo su daga mimbari.
Sheikh Albaniy ya ce a shirye ya ke domin daukar mataki saboda kullum sai ya yi atisaye kafin fitowa daga cikin gidansa.
Asali: Legit.ng