Hukumar DSS Ta Kama Wanda Ya Sace Mahaifiyar Rarara, an Samu Miliyoyi
- Rahotanni sun tabbatar da cewa hukumar DSS a jihar Kano ta tabbatar da cewa ta cafke wani da hannu a sace mahaifiyar Dauda Rarara
- Hukumar ta kai samame ne dajin Makarfi inda ta samu masu garkuwan suna raba kudin fansa da suka karba daga jama'a
- Wannan na zuwa ne bayan sace mahaifyar Rarara a jihar Katsina kafin ta samu nasarar kubuta bayan shafe makwanni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi nasarar cafke wanda ake zargi da sace mahaifiyar Dauda Kahutu Rarara.
Hukumar a jihar Kano ta cafke mutumin ne yayin wani samame inda ta yi ajalin wani daga cikin wadanda ake zargin.
Rarara: DSS ta kama wani da ake zargi
Daily Trust ta tattaro cewa hukumar ta kai samame ne a dajin Makarfi inda suke raba kudin fansa da suka karba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya ta tabbatar da cewa hukumar ta yi nasarar samun N26.5m a wurin masu garkuwa yayin samamen, cewar Daily Post.
Majiyar ta ce hukumar da ke Kano ta kai samame bayan samun bayanan sirri inda ta afkawa wasu mutane biyar a cikin dajin yayin da suke raba kudin fansa.
Rarara: Yadda aka kama Hamisu a Kano
"Wani Hamisu Tukur yana hannun jami'an tsaro da raunuka da kuma harbin bindiga a jikinsa."
"Sannan wani mai suna Bature ya rasa ransa yayin samamen da aka kai."
- Cewar majiyar
Wannan na zuwa ne bayan sace mahaifiyar fitaccen mawakin siyasaa kauyen Kahutu da ke karamar hukumar Danja a jihar Katsina.
Dattijuwar ta shafe akalla kwanaki 20 a hannun 'yan bindiga wadanda suka nemi N900m a matsayin kudin fansa.
'Yan bindiga sun sako mahaifiyar Rarara
A wani labarin, kun ji cewa 'yan bindiga sun sako mahaifiyar fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara bayan shafe akalla kwanaki 20 a tsare.
Tun farko 'yan bindigan sun bukaci a biya su kudin fansa har N900m sai dai ba a sani ba ko biyan kudin ne sanadin sake dattijuwar ba.
Hakan ya biyo bayan harin 'yan bindiga inda suka kutsa sabon gidan Rarara da ke Kahutu a ƙaramar hukumar Ɗanja inda suka sace mahaifiyarsa.
Asali: Legit.ng